A karon farko, mutane uku sun warke daga cutar covid-19 a Kano

A karon farko, mutane uku sun warke daga cutar covid-19 a Kano

An sallami mutum uku da ke jinyar cutar covid-19 bayan sun warke a jihar Kano, kamar yadda ma'aikatar lafiya ta jihar ta sanar a ranar Laraba.

Wanan shine karo na farko da aka samu labarin warkewar wani mai dauke da kwayar cutar coronavirus a jihar Kano.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ma'aikatar lafiya a Kano ta fitar ranar Laraba a shafinta na tuwita.

Ya zuwa yanzu adadin ma su dauke da cutar coronavirus ya kai mutum 397, a cewar ma'aikatar.

A cewar ma'aikatar, an samu karin sabbin mutane 32 da annobar ta harba ranar Talata a jihar Kano.

Hukumar yaki da cututtuka ma su yaduwa a kasa (NCDC) ta ce annobar cutar covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 148 a fadin Najeriya.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da NCDC ta fitar da misalin karfe 11:45 na daren ranar Talata, 05 ga watan Mayu, 2020.

DUBA WANNAN: A karshe, ministan lafiya ya bayyana magananin da FG ta amince da amfani da shi a kan ma su jinyar covid-19

A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na tuwita, ta sanar da cewa karin sabbin mutane 148 din sun fito daga jihohin Najeriya kamar haka;

43-Lagos

32-Kano

14-Zamfara

10-FCT

9-Katsina

7-Taraba

6-Borno

6-Ogun

5-Oyo

3-Edo

3-Kaduna

3-Bauchi

2-Adamawa

2-Gombe

1-Plateau

1-Sokoto

1-Kebbi

NCDC ta ce ya zuwa karfe 11:45 na daren ranar Talata, 05 ga watan Mayu, akwai jimillar mutane 2950 da aka tabbatar da cewa suna dauke da kwayar cutar covid-19 a Najeriya.

An sallami mutane 481 bayan an tabbatar da samun saukinsu, a yayin da cutar ta hallaka jimillar mutane 98.

Duk da alkaluman NCDC na ranar Talata sun nuna an kara samun raguwar adadin mutanen da cutar ta harba, har yanzu rahotanni na cigaba da kawo labaran mutuwar mutane, musamman a jihohin arewa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel