Kasashe 5 da cutar korona ta bulla amma ba a rasa rai ba

Kasashe 5 da cutar korona ta bulla amma ba a rasa rai ba

Zuwa ranar yau Laraba, 6 ga watan Mayu, a kalla mutum miliyan 3.6 suka kamu da cutar coronavirus a fadin duniya. An samu warakar mutum 1.2 amma an rasa rayuka 252,000 a fadin duniya.

Tun bayan bullowar cutar a Najeriya, mutum 2,950 ne suka kamu da cutar yayin da mutum 481 ne suka warke daga jinyar cutar. Mutum 98 ne suka rasa rayukansu.

Cutar sarkewar numfashin wacce aka fara samu a garin Wuhan a kasar China ta bulla a kalla kasashe 180 na duniya.

Covid-19: Kasashe 5 da cutar korona ta bulla amam ba a rasa rai ba

Covid-19: Kasashe 5 da cutar korona ta bulla amam ba a rasa rai ba
Source: UGC

Akwai wasu kasashen da har yanzu ba a samu bullar cutar ba amma kuma wasu har ta bulla bata kashe ko rai daya ba. Ga wasu daga cikin kasashen.

KU KARANTA KUMA: Matafiya 4 cikin 11 da aka damke za su shiga kudu daga Sokoto suna dauke da Korona

1. Tsibirin Falkland: An tabbatar da cewa mutum 13 sun kamu da cutar amma duk sun warke.

2. Greenland Greelnad: Ita ce kasa mai tsibiri mafi girma a duniya. Tana tsakanin kogin Arctic da na Atlantic. Mutum 11 ne suka kamu amma duk sun warke. Har yanzu kuwa ba a sake samun mai cutar a kasar ba.

3. Papua New Guinea: Cutar ta harba mutum 8 amma dukkansu sun warke. Kasar na kudu maso yay kogin Pacific. An fara samun bullar cutar a kasar a ranar 20 ga watan Maris.

4. Saint Barthelemy: Kasar ta tabbatar da kamuwar mutum 6 da cutar amma duk sun warke a halin yanzu. Tsibiri ne wanda aka fi sani da St. Barts. Yana da gabobin ruwa da kuma shaguna masu matukar bada sha'awa.

5. Anguilla: Kasar ta tabbatar da kamuwar mutum 3 da muguwar cutar amma a halin yanzu duk sun warke. Kasar na nahiyar Amurka ta Arewa.

A wani labarin kuma, ministan lafiya, Dakta Osagie Ehanire, ya ce Najeriya ta fara amfani da wani magani mai suna 'remdesivir' a kan ma su jinyar cutar covid-19.

Da ya ke gabatar da jawabi a gaban mambobin majalisar wakilai ranar Talata, Ehanire ya ce da maganin ake amfani a kan ma su jinyar cutar covid-19 jihar Legas.

Sai dai, ministan bai bayyana irin tasirin maganin a kan cutar covid-19 ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel