Matafiya 4 cikin 11 da aka damke za su shiga kudu daga Sokoto suna dauke da Korona

Matafiya 4 cikin 11 da aka damke za su shiga kudu daga Sokoto suna dauke da Korona

An samu matafiya hudu a cikin 11 da yan sandan jihar Oyo suka kama a hanyarsu ta zuwa Akure daga jihar Sokoto a karshen mako dauke da cutar COVID-19.

Manajan kula da lamarin a jihar Oyo, Dr Taiwo Ladipo ne ya bayyana hakan a ranar Talata.

A cewarsa, a yanzu haka an killace mutum hudun da aka tabbatar suna dauke da cutar a wajen killace masu ita da ke Olodo.

Wani mamba a kwamitin yaki da COVID-19, Farfesa Temitope Alonge, ma ya tabbatar da lamarin ga Channels TV. Ya ce an kwantar da masu cutar a cibiyar killace masu korona da ke Olodo domin samun kulawar likitoci.

Matafiya 4 cikin 11 da aka damke za su shiga kudu daga Sokoto suna dauke da Korona

Matafiya 4 cikin 11 da aka damke za su shiga kudu daga Sokoto suna dauke da Korona
Source: UGC

Adadin masu korona da aka tabbatar a jihar zuwa ranar Talata ya kai 39, inda 28 ke nan da ita a yanzu haka.

A safiyar ranar Laraba, hukumar yaki da hana yar’uwa cututtuka ta Najeriya (NCDC) ta sanar da cewar ba a sake samun wasu masu cutar ba a jihar.

Zuwa yanzu an sallami mutum tara yayinda mutum biyu suka mutu.

KU KARANTA KUMA: An shiga zullumi bayan alamomin cutar COVID-19 ta kashe wasu mutum 4 a wata jihar arewa

A wani labarin kuma, mun ji cewa kungiyar likitocin Najeriya na reshen jihar Kogi sun nuna damuwarsu a game da kin yi wa mutanen da ake zargin ba su da lafiya gwajin cutar COVID-19.

A ranar Talatar nan, an yi wa mutane kusan 20, 000 gwajin kwayar cutar COVID-19 a fadin Najeriya.

Jihar Kogi ta na cikin inda har yanzu ba a samu labarin wani mai dauke da cutar ba. A jihar Kogi, gwamnati ta na hana ayi wa Bayin Allah gwajin cutar COVID-19 da gan-gan.

Gwamnatin jihar ta ma fito ta na kukan ana kokarin tabbatar da samun mai cutar a jihar.

Wannan zargi da gwamnatin Kogi ta ke yi na cewa wasu na neman kakaba mata Coronavirus ya jefa likitocin da ke aiki a jihar cikin wani hali, har ta kai kungiyar NMA ta fito ta yi magana.

Shugaban Kungiyar likitocin kasar na reshen jihar watau Dr. Kabir Zubair ya gargadi gwamnatin Yahya Bello game da matakin da ta dauka, ya ce abin da gwamnatin ta ke yi ya na da hadari.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel