Sanatoci sun shawarci Buhari game da yadda ya kamata ya sauya aikin Yansanda

Sanatoci sun shawarci Buhari game da yadda ya kamata ya sauya aikin Yansanda

Majalisar dattawan Najeriya ta yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fasa rundunar Yansandan Najeriya a wani mataki na yi mata garambawul don inganta aikin ta.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya,NAN, ta ruwaito majalisar ta ce haka zai kara ma rundunar karfin, zai kara ma aikin Yansanda kima da kuma taimaka wajen tsaron al’ummar kasar.

KU KARANTA: Za’a gudanar da gwajin COVID-19 a kan yan kwallon Barcelona kafin La Liga ta cigaba

Hakan na daga cikin shawarwarin da kwamitin wucin gadi da majalisar ta kafa domin ya yi nazari game kalubalen tsaro a Najeriya tare da samar da mafita daga matsalolin tsaro a kasar.

A ranar 29 ga watan Janairu ne majalisar ta kafa kwamitin a karkashin jagorancin jagoran majalisar Sanata Yahaya Abdullahi daga jahar Kebbi.

Kum tuni majalisa ta amince da rahoton kwamitin kamar yadda kakaakin majalisar, Sanata Ajibola Basiru ya bayyana.

Kakaakin majalisar ya bayyana cewa kwamitin ta bayar da shawarwari da dama masu muhimmanci matuka ga majalisar, kuma majalisar ta amince dasu duka a ranar Talata.

Daga cikin shawarwarin akwai;

Majalisa ta nemi shugaban kasa ya umarci ma’aikatar kula da aikin Yansanda da babban sufetan Yansanda su raba aikin rundunar ta hanyar ma rundunar karfi a shiyyoyin kasar.

Kwamitin ta nemi gwamnatin Buhari ta kafa kwamitin bada shawari game da tsaro a matakin shiyya shiyya na Najeriya don bada shawara game da matsalolin tsaron da suka addabi shiyyar.

Ta nemi Buhari ya kafa majalisar tsaro a shiyyoyi da zai kunshi AIG na shiyyar, kwamishinonin Yansanda da kuma sauran shuwagabannin hukumomin tsaro dake shiyyar.

Sauran sun hada da shugaban sarakunan gargakiyan shiyyar, kungiyoyin addinai, kungiyoyi masu zaman kansu, wakilan Sanatoci da na yan majalisu da dai sauransu.

Sa’annan kwamitin ta nemi shugaban kasa ya umarci babban sufetan Yansanda ya kaddamar da aikin Yansandan unguwanni tare da hadin gwiwar masu ruwa da tsaki.

Majalisar ta shawarci majalisun jahohi su samar da dokokin da zasu halasta aikin Yansandan unguwanni, sa’annan gwamnoni su samar da isassun kudade ga Yansandan unguwanni.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel