Majalisa za ta yi bincike kan zargin badakala da barna a Ma'aikatar NDDC

Majalisa za ta yi bincike kan zargin badakala da barna a Ma'aikatar NDDC

- ‘Yan Majalisar Tarayya za su yi bincike game da aikin Ma’aikatar NDDC

- Majalisar kasar ta na zargin ana sabawa doka da ka’idar aiki a Ma’aikatar

- Ana zargin Ma’aikatar da facakar kudi da daukar wadanda ba su dace ba

Majalisar wakilan tarayya za ta fara gudanar da bincike na musamman a game da zargin da ta ke yi na cewa an tafka badakala a hukumar NDDC mai kula da cigaban yankin Neja-Delta.

‘Yan majalisar tarayyar sun aikawa ministan harkokin Neja-Delta, Godswill Akpabio da ‘yan kwamitin rikon kwaryar NDDC takarda inda su ke gayyatarsu domin amsa tambayoyi.

Ma’aikatar Neja-Delta ta na karkashin sanata Godswill Akpabio wanda tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom ne. Majalisar ta na zargin an wawuri wasu makudan kudi a hukumar NDDC.

An bukaci kwamitin da ke sa ido a kan harkokin Neja-Delta a majalisar wakilai ya binciki zargin satar dukiyar gwamnati musamman Naira biliyan 40 da aka kashe a cikin watanni biyu.

KU KARANTA: Ministan lafiya ya yi magana game da maganin cutar COVID-19

Majalisa za ta yi bincike kan zargin badakala da barna a Ma'aikatar NDDC
Hoton 'Yan Majalisa bayan sun dawo aiki daga shafin Tuwita
Asali: Twitter

Majalisa ta ba wannan kwamiti damar gudanar da wannan bincike, sannan ya gabatar da rahoto. ‘Yan majalisar sun ci ma matsaya ne yayin da Peter Akpatason ya kawo maganar a jiya.

‘Ya ‘yan kwamitin za su yi binciken kurilla, su bi kadin duk wasu kudi da aka kashe da kaya da aka saya a karkashin hukumar NDDC a cikin wannan shekarar, su gano ko an bi doka.

Jaridar Daily Trust ta ce kwamitin zai yi bincike game da yadda ake daukar ma’aikata a NDDC domin tabbatar da cewa ba a saba dokar da ta bada damar kafa ma’aikatar tun farko ba.

Dalilin haka ne majalisar wakilan ta yanke hukuncin kiran Godswill Akpabio da shugabannin NDDC na rikon kwarya domin su yi wa ‘yan Najeriya bayanin aikin da su ke yi a yankin.

‘Yan majalisar sun ce su na ta samun korafi ta kafafen zamani da wasiku har daga ‘yan kwangila da masu ta=cewa a Neja-Delta game da yadda hukumar NDDC ta ke daukan bara-gurbi aiki.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel