An kama almajirai sama da guda 100 a Abia, an mayar da su gida

An kama almajirai sama da guda 100 a Abia, an mayar da su gida

Sama da almajirai 100 ne jami'an tsaro a jihar Abia suka tsare a ranar Talata, 5 ga watan Mayu, a kan iyakar Abia zuwa Enugu. Jami'an sun gaggauta mayar da su inda suka fito.

A yayin bayyana hakan ga manema labarai, kwamishinan yada labarai, Chief John Okiyi-Kalu ya ce almajiran sun koma inda suka fito sakamakon rufe iyakar jihar da aka yi.

An gano cewa, an tsare wasu almajirai da aka boye a wata babbar motar da ke shiga jihar daga yankin Arewa cin kasar nan.

An kama almajirai sama da guda 100 a Abia, an mayar da su gida
An kama almajirai sama da guda 100 a Abia, an mayar da su gida
Asali: UGC

Hukumar tsaro wacce kwamishinan tsaro na jihar, Prince Dan Okoli ke jagoranta, ta tsare almajiran ne a iyakokin Abia da Enugu a kan babban titin Enugu zuwa Fatakwal.

Kamar yadda Okiyi Kalu ya bayyana, "mun mayar da manyan motocin abinci da almajirai masu tarin yawa da suka boye a ciki. Mun hana su tsallakowa iyakar jihar.

"Mun tuntubi 'yan arewan da ke da kusanci da iyakar kuma sun ce za su mayar dasu duk inda suka fito.

"Ba mu son killace kowa saboda bai kamata su zo nan ba. Duk da babu wata dokar da ta hana su shiga jihar."

KU KARANTA KUMA: Cika shekaru 10 da mutuwa: Abin da Buhari ya fada a kan marigayi Yar'adua

Kamar yadda jaridar Sunnews Online ta ruwaito, kwamishinan ya bayyana cewa, gwamnan jihar ya umarci kara jami'an tsaro a kan iyakokin jihar da Akwa Ibom don ci gaba da tabbatar da babu wanda ya shigo jihar.

A wani labarin kuma mun ji cewa, Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa ya bukaci jama'a da su kiyaye lafiyar majinyatansu da tsofaffi wadanda shekarunsu suka kai 65 ko sama da haka ta hanyar tabbatar da sun zauna a gida.

Hakan wani yunkuri ne na hana su kamuwa da cutar coronavirus wacce ta mamaye kasashe duniya ciki harda Najeriya.

Kamar yadda jaridar The Nation ta bayyana, gwamnan ya haramta taron shakatawa ko na addinai amma banda na biki da jana'iza. Su ma kada taron ya fi na mutum 15.

Duk wadannan dokokin na daga cikin tarin umarnin da gwamnan ya saka hannu a kai a ranar Talata a matsayin sharuddan sassauta dokar hana zirga-zirga ta jihar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel