Gwamnatin Adamawa ta saka dokar kulle a kan dattijai

Gwamnatin Adamawa ta saka dokar kulle a kan dattijai

Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa ya bukaci jama'a da su kiyaye lafiyar majinyatansu da tsofaffi wadanda shekarunsu suka kai 65 ko sama da haka ta hanyar tabbatar da sun zauna a gida.

Hakan wani yunkuri ne na hana su kamuwa da cutar coronavirus wacce ta mamaye kasashe duniya ciki harda Najeriya.

Kamar yadda jaridar The Nation ta bayyana, gwamnan ya haramta taron shakatawa ko na addinai amma banda na biki da jana'iza. Su ma kada taron ya fi na mutum 15.

Duk wadannan dokokin na daga cikin tarin umarnin da gwamnan ya saka hannu a kai a ranar Talata a matsayin sharuddan sassauta dokar hana zirga-zirga ta jihar.

Dokokin, wadanda aka bayyana ga manema labarai a yammacin Talata, sakataren yada labarai na gwamnan, Humwashi Wonosikou ya goyi bayan amince wa da komawar ma'aikatan bakin aiki.

Ma'aikatan gwamnati a mataki na 12 ko sama da haka ne za su koma bakin aikin amma a kungiya kashi biyu a kowacce ma'aikata.

Gwamnatin Adamawa ta saka dokar kulle a kan dattijai
Gwamnatin Adamawa ta saka dokar kulle a kan dattijai
Asali: UGC

Dokar ta ce jami'an da ke aiki na musamman basu cikin wadanda dokar ta hau kansu.

Amma dole ne su kiyaye dokar nisantar juna, saka takunkumin fuska a kowanne lokaci, duba dumin jikinsu akai-akai da wanke hannu.

Dokar ta bada goyon baya ga kulle manyan kasuwannin shanu na Mubi, Ganye, Maiha da sauran manyan garuruwan da ke fadin jihar.

Masu adaidata sahu kuwa an amince su dauka mutum uku ne har da matukin. Masu mota kirar bas za su iya daukar mutum hudu tak.

KU KARANTA KUMA: Yarinya yar shekara 6 ta kamu da cutar Coronavirus a jahar Jigawa

Dokar ta kara da bayyana cewa, ababen hawa da ke dauke da kayan noma, kayayyakin man fetur, kayayyakin asibiti da na tallafi ne kadai za a amince su shiga jihar.

Dokar ta ce makarantun jihar za su kasance a garkame har sai yadda ta kama. Amma gwamnatin na goyon bayan koyar da dalibai ta yanar gizo.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel