Cika shekaru 10 da mutuwa: Abin da Buhari ya fada a kan marigayi Yar'adua

Cika shekaru 10 da mutuwa: Abin da Buhari ya fada a kan marigayi Yar'adua

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kwatanta marigayi tsohon shugaban kasa Umaru Musa Yar'adua da ma'aikacin gwamnati mai gaskiya da rikon amana.

A sakon ta'aziyyar marigayin na ranar zagayowar mutuwarsa karo na 10, shugaban kasa Buhari ya kwatanta marigayin da mutum mai kishin kasa wanda ya mayar da hankali wajen rage radadin talakan Najeriya.

Kamar yadda shugaban kasar ya bayyana, duk da banbancin siyasar da ke tsakaninsa da marigayin, yana matukar ganin kimarsa a matsayin shugaban da ya matukar bautawa kasa a tarihin Najeriya.

Cika shekaru 10 da mutuwa: Abin da Buhari ya fada a kan marigayi Yar'adua

Cika shekaru 10 da mutuwa: Abin da Buhari ya fada a kan marigayi Yar'adua
Source: UGC

Kamar yadda jaridar The Nation ta bayyana, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika sakon ta'aziyyarsa ga iyalan marigayin da gwamnatin jihar Katsina.

Ya yi kira ga 'yan siyasar kasar nan da su yi koyi da kyawawan dabi'u tare da halayyar shugaban.

"Duk da banbancin siyasa da ke tsakaninmu, shugaba Yar'adua babu shakka yana cikin shugabannin talakawa masu matukar kishin kasa.

"Dole ne a jinjinawa kowanne shugaba da ya cancanta, ko da baku kasance a bangaren siyasa daya ba, zan iya cewa tarihi ba zai taba mantawa da mutum mai gaskiya da rikon amana kamarsa ba da ya bautawa kasarsa.

"A yayin da muke tunawa da shugaba Yar'adua a yau, ina kira garemu da mu yi koyi da hakuri tare da sanyin halinsa. Hakan ne zai sa mu dage ba tare da mun gurbata kasarmu da siyasar gaba ba.

"Ina amfani da wannan damar wajen mika ta'aziyyata da addu'o'in fatan alheri ga iyalansa da gwamnatin jihar Katsina. Allah ya ci gaba da yi masa rahama da gafara."

KU KARANTA KUMA: Shugaban NNL kuma mamba a FA ya fadi, ya mutu a take

Ku tuna cewa a rana mai kaman ta yau ne, 5 ga watan Mayu, amma shekaru goma da suka gabata ne tsohon shugaban Najeriya, Umaru Musa Yar’ Adua ya rasu a kan mulki.

Duk da cewa shekaru uku kawai ya yi a kan mulki gwamnatinsa ta dukufa wurin aiwatar da wasu ayyuka da tsare tsare inda wasu daga cikinsu an kammala su.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel