Ganduje ya nada sabon sarkin masarautar Rano a Kano

Ganduje ya nada sabon sarkin masarautar Rano a Kano

- Gwamna Ganduje ya amince da nadin, Kabiru Inuwa, hakimin karamar hukumar Kibiya, a matsayin sabon sarkin Rano

- Sakataren gwamnatin Kano, Alhaji Usman Alhaji, ya ce Inuwa na daga cikin sunayen mutane uku da ma su nada sarki a masarautar Rano su ka aikawa gwamna Ganduje

- Masarautr Rano ta na daya daga cikin sabbin masarautu hudu da gwamna Ganduje ya kirkira a jihar Kano

Gwamnatin jihar Kano ta amince da nadin hakimin karamar hukumar Kibiya, Kabiru Inuwa, a matsayin sabon sarkin masarautar Rano.

Sakataren gwamnatin jihar Kano, Alhaji Usman Alhaji, ne ya sanar da hakan da yammacin ranar Talata yayin wata ganawarsa da manema labarai a Kano.

Alhaji ya ce Inuwa na daya daga cikin sunayen mutane uku da ma su alhakin nada sarki a masarautar su ka aikowa gwamnatin jiha.

Sauran mutane biyu da aka aiko da sunayensu su ne; Muhammadu Umar; hakimin karamar hukumar Bunkure da Munir Abubakar; chiroman Rano.

Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bukaci sabon sarkin ya kasance mai jajircewa wajen tabbatar da adalci a tsakanin talakawansa.

Ganduje ya nada sabon sarkin masarautar Rano a Kano
Marigayi tsohon sarkin Rano
Asali: Twitter

A ranar Asabar, 02 ga watan Mayu, ne Allah ya yi wa tsohon sarkin Rano, Tafida Abubakar Ila (Autan bawo), rasuwa. Ya rasu ya na da shekaru 74 a duniya.

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga ma su hijabi sun saki basarake Abdullahi Magaji bayan biyan kudin fansa

A ranar Juma'a, 01 ga watan Mayu, aka kwantar da tsohon sarki Ila a asibitin koyarwa na Malam Aminu (AKTH) da ke birnin Kano bayan ya kamu da wata rashin lafiya da ba a bayyanata ba.

Dag bisani an mayar da shi asibitin kwararru da ke Nasarawa a birnin Kano, inda ya mutu washegari, ranar Asabar.

Masarautr Rano na daya daga cikin sabbin masarautu hudu da gwamna Ganduje ya kirkira a jihar Kano.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel