An bayyana dalilin da ya sa likitoci 10 su ka kamu da cutar covid-19 a AKTH Kano
- A ranar Talata ne rahotanni su ka bayyana cewa wasu likitoci da ma'aikatan lafiya a Kano sun kamu da kwayar cutar covid-19
- Shugaban likitocin da ke aiki a asibitin koyarwa na AKTH da ke Kano, Dakta Abubakar Nagoma, ya alakanta faruwar hakan da rashin gaskiya daga bangaren marasa lafiya
- Dakta Abubakar ya ce kwanan nan likitocin asibitin za su daina duba marasa lafiya matukar ba a samar mu su da isassun kayan kare kai ba (PPEs)
Shugaban kungiyar likitocin da ke aiki a asibitin koyarwa na AKTH da ke Kano, Dakta Abubakar Nagoma, ya ce marasa lafiya da ke ziyartar asibitin ba sa son fadin gaskiya yayin bayar da bayanansu.
A yau, Talata, ne rahotanni su ka bayyana cewa wasu likitoci 10 a Kano sun kamu da kwayar cutar covid-19 yayin da su ke aikinsu na kula da lafiyar jama'a.
Dakta Nagoma ne ya sanar da hakan ga manema labarai, kamar yadda jaridar The Sun ta rawaito.
Ya shaidawa manema labarai cewa ma'aikatan lafiyar sun kamu da kwayar cutar ne yayin da su ke kan aikinsu, ya kara da cewa daga cikin ma'aikatan lafiyar akwai manyan likitoci.
Yanzu haka an mayar da 8 daga cikin likitocin cibiyar killacewa ta Kano, yayin da sauran biyun su ka killace kansu a gidjensu, a cewar Dakta Nagoma.
DUBA WANNAN: 'Yan bindiga ma su hijabi sun saki basarake Abdullahi Magaji bayan biyansu kudin fansa
Likitan ya ce an gwada dukkan likitocinsu 100 a makon jiya, inda ya alakanta kamuwarsu da kwayar cutar da rashin bayar da bayanai na gaskiya daga wurin marasa lafiya.
Ya kara da cewa wasu daga cikin marasa lafiyar da ke ziyartar asibitin su na rufe fuska da takunkumi don kar a yi zargin su na dauke da kwayar cutar covid-19 ko basa bin matakan kare kai.
A cewar Nagoma, likitocin asibitin ba su da wadatattun kayan kare kansu (PPEs) tare da yin barazanar cewa za su daina duba marasa lafiya matukar ba a kawo mu su isassun kayan aiki ba.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng