WHO: Ya kamata ayi bincike kafin a fara amfani da magugunan gargajiyan COVID-19

WHO: Ya kamata ayi bincike kafin a fara amfani da magugunan gargajiyan COVID-19

- Hukumar lafiya ta Duniya ta yi magana a kan amfani da magugunan gargajiya

- Wasu su na ikirarin sun gano maganin gargajiyan da ke warkar da Coronavirus

- WHO ta bada shawarar a jira a tabbatar da inganci da illar wadannan maguguna

A jiya ranar Litinin, 4 ga watan Mayu, 2020, hukumar lafiya ta Duniya, WHO, ta fito ta ja hankali game da masu amfani da wasu itatuwa da sunan cewa su na maganin cutar Coronavirus.

A wani jawabi da hukumar ta fitar, ta bayyana cewa ko da ta na goyon bayan magungunan gargajiya, akwai bukatar ayi bincike a kan illar magugunan kafin mutane su fara shansu.

Ganin cewa kasar Madagascar ta kirkiro wani magani, WHO ta ce akwai bukatar ayi bincike a tabbatar da karfin duk maganin da aka kirkira daga itatuwa domin sanin ko su na aiki.

Shugaban Madagascar, Andry Rajoelina, ya kaddamar da wani magani da ya ce sun gano wanda ke warkar da cutar COVID-19, tuni wasu kasashen Afrika su ka fara amfani da maganin.

KU KARANTA: Annobar COVID-19 ba ta dakatar da yaki da Barayi a Najeriya ba

Duk da cewa har yanzu babu wanda ya yi bincike a kan maganin kuma ya tabbatar da ingancinsa, wasu su na ta faman sayen magani daga Madagascar, su na jarraba sa'arsu.

“Hukumar WHO ta yarda cewa magungunan gargajiya su na da tarin amfani, kuma Afrika ta na ta na da tsohon tarihi na amfani da magungunan gargajiya wajen warkar da jama’anta.”

Jawabin ya kara da cewa: “Ana sa ran itatuwa irinsu Artemisia annua su na kunshe da sinadaran da za su iya maganin COVID-19, kuma ayi bincike domin gano illarsu da karfin aikinsu.”

Jaridar Premium Times ta ce daga jawabin za a fahimci cewa hukumar WHO ta na ganin ya na da matukar muhimmanci a fara binciken lafiyar magani kafin mutane su fara kwankwada.

Tun ba yau ba WHO ta dade ta na bada gudumuwa wajen kirkiro magungunan gargajiya daga saiwar itatuwa. Hukumar lafiyar ta kan yi bincike kan inganci da haduran amfani da su.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel