Hon. Soro ya rabawa manyan APC da mabukata kudi da abinci a Darazo da Ganjuwa

Hon. Soro ya rabawa manyan APC da mabukata kudi da abinci a Darazo da Ganjuwa

- Mansur Soro ya raba buhunan abinci ga wadanda ba su da karfi a Yankinsa

- ‘Dan majalisar ya kuma raba kudi ga shugabannin APC na Darazo/Ganjuwa

‘Dan majalisar wakilan tarayya mai wakiltar yankin mazabar Darazo da Ganjuwa na jihar Bauchi, Mansur Manu Soro ya yi wa mutanensa da ‘ya ‘yan jam’iyyar APC abin alheri.

Honarabul Mansur Manu Soro ya rabawa shugabannin jam’iyyarsa ta APC na kananan hukumomin Darazo da Ganjuwa kudi Naira miliyan daya a karshen makon jiya.

Bayan haka, ‘dan majalisar ya raba kayan abinci wanda su ka hada da buhuna 700 na shinkafa da taliya ga marasa karfi. Ya yi wannan ne domin rage masu radadin da su ke ciki.

Wani babban hadimin ‘dan majalisar mai suna Saidu Abdu Sade ne ya wakilce shi a wurin bikin rabon kayan alherin. Jaridar Daily Trust ta ce an yi rabon abincin ne ranar Lahadi.

KU KARANTA: Dino Melaye ya yi wa 'Yan siyasa kudin goro, ya ce duk sun gaza

Hon. Soro ya rabawa manyan APC kudi da abinci a Darazo da Ganjuwa

Honarabul Manu Soro lokacin da ya mike ya na jawabi a Majalisa
Source: Twitter

Mansur Soro ya shirya wannan agaji ne ga marasa karfi a daidai wannan lokaci da annobar cutar COVID-19 ta ke durkusar da kasuwanci da hanyoyin neman abincin Bayin Allah.

Da Malam Saidu Abdu Sade ya ke magana a madadin Hon. Mansur Manu Soro, ya bayyana cewa: “Mu na harin mutane 7, 000 ne daga cikin mazabu 22 da ke Darazo da Ganjuwa.”

Kwanaki ‘dan majalisar ya kaddamar da shirin gina wasi asibitocin kananan yara a Soro da Sade. Da ake fara wannan aiki, Soro ya yi kira ga jama’a su kare kansu daga COVID-19.

Idan ba ku manta ba wani sanatan Kaduna, Uba Sani ya rabawa mutanensa kayan abincin azumi a makonnin da su ka wuce. Sanatan ya kashe miliyoyi wajen bada wannan agaji.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng News

Online view pixel