'Yan bindiga sanye da hijabi sun saki basarake Abdullahi Magaji bayan biyan kudin fansa

'Yan bindiga sanye da hijabi sun saki basarake Abdullahi Magaji bayan biyan kudin fansa

Abdullahi Magaji, basarake mai daraja ta biyu a jihar Nasarawa, ya shaki iskar 'yanci bayan wasu 'yan bindiga sanye cikin hijabi sun sace shi ranar Alhamis da ta gabata.

'Yan bindigar, wadanda su ka sace Magaji a gidansa, sun sake shi bayan an biyasu kudin fansa da ba a bayyana adadinsu ba.

Bayan sun sace shi, 'yan bindigar sun tuntubi iyalinsa tare da neman miliyan N50 a matsayin kudin fansa kafin su sake shi.

Jaridar Daily Nigerian ta rawaito cewa an saki basarake Magaji da misalin karfe 8:00 na safiyar yau, Talata.

An samu basaraken a yankin Kiguna mai nisan kilomita 24 daga gidansa da ke Lafia, babban birnin jihar Nasarawa.

'Yan bindiga ma su hijabi sun saki basarake Abdullahi Magaji bayan biyan kudin fansa
Abdullahi Magaji Hoto: Daily Nigerian
Source: UGC

Akwai alamun gajiya a tattare da basaraken yayin da wakilin jaridar Daily Nigerian ya ziyarce shi.

A wani labari da jaridar Daily Trust ta wallafa a ranar Litinin, 04 ga watan Mayu, ta bayyana cewa an rufe fadar masarautar Daura bayan samun bullar annobar covid-19.

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, dan asalin karamar hukumar Daura ne.

DUBA WANNAN: Sojoji sun kama manyan 'yan leken kungiyar Boko Harm 16, sun kashe mayaka 134

Sakataren gwamnatin jihar Katsina, Dakta Mustapha Inuwa, ya tabbatar da rufe fadar sarkin tare da bayyana cewa sakamakon gwajin da ake jira ne kadai zai nuna lokacin da za a bude fadar.

"Ba wani sabon abu bane, haka tsarin ya ke duk duniya, matukar an samu mai dauke da kwayar cutar covid-19. An rufe fadar yayin da aka dauki jinin mutane zuwa cibiyar gwaji," a cewarsa.

Da ya ke magana a kan lamarin, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isa, ya ce, "mu dama a wurin rundunar 'yan sanda, karamar hukumar Daura a rufe ta ke, hakan kuma ya shafi kowanne lungu da sako da kuma kowanne gida.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel