Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya jinjinawa marigayi Yar’Adua

Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya jinjinawa marigayi Yar’Adua

Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, ya jinjinawa marigayi tsohon shugaban kasa Umar Musa Yar’adu, shekaru goma bayan mutuwarsa.

A yau Talata, 5 ga watan Mayu 2020, ne marigayi Yar’Adua ya cika shekaru 10 da rasuwa. Marigayin ya rasu ne bayan wata 'yar doguwar jinya da ya yi a lokacin ya na kan karagar mulki.

Goodluck ya wallafa sakon jinjinawar ne a shafnsa na Facebook, inda ya bayyana cewa Yar’Adua ya yi rayuwa sannan ya mutu wajen yi wa kasarsa hidima.

Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya jinjinawa marigayi Yar’Adua

Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya jinjinawa marigayi Yar’Adua
Source: UGC

Ga cikakken jawabin da ya wallafa a shafin nasa:

"Shekaru goma kenan da mutuwar mai girma shugaban kasa Umar Musa Yar’Adua. A wannan rana, duk shekara, zukatanmu kan cika da tunaninsa saboda jajircewarsa da kuma halayensa na kwarai.

"Ya kasance shugaba da babu tamkarsa wanda ya yi rayuwa sannan ya mutu domin kasarsa. Ya tsaya tsayin daka ta bangaren al’ummansa, yana wahala dare da rana domin inganta rayuwarsu.

"Shugaba Yar’Adua ya gina karfafan buri, soyayya da fahimta wanda a kansu ne ya zama jigon hadin kan kasa da kuma kawo sauyi mai inganci a fadin kasarmu mai albarka.

"Ta bangarori da dama ya tsaya-tsayin daka. Mutum ne mai dadin zama da tarin alkhairi wanda ke ta kokarin karfafa dangantakar kasarmu; ta haka ne ya bar wa magadansa aikin tabbattar da kudirinsa.

"Shakka babu shugaba Yar’Adua ya bar tarihi duba ga yadda ya dukufa a kan tafarkin damokradiyya, mutunta yancin mutane da kuma jajircewarsa wajen aiki da doka da kuma adalci.

"Zan ci gaba da tuna Yar’Adua a matsayinsa na abokin aiki kuma ubangida wanda ya zama dan’uwana kuma aboki."

Ku tuna cewa marigayi Yar'adua shine shugaba na biyu da ya karbi ragamar mulkin kasar bayan komawarta ga turbar damokradiyya a shekarar 1999.

KU KARANTA KUMA: Badakala: Jam’iyyar PDP ta jefi Yemi Osinbajo da laifin wawurar kudi a NEMA

Kuma ya karbi ragamar mulki ne daga hannun shugaba Olusegun Obasanjo bayan wani zabe mai cike da takaddama a shekarar 2007.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel