‘Dan wasa Lionel Messi zai kai shekaru kusan 40 a Duniya ya na kwallo - Xavi

‘Dan wasa Lionel Messi zai kai shekaru kusan 40 a Duniya ya na kwallo - Xavi

- Xavi ya ce Lionel Messi zai iya cigaba da kwallo har ya kai shekara 40

- Kocin ya na ganin cewa Messi ya na da sauran shekaru a gida da waje

Fitaccen ‘dan kwallon nan da aka yi a kungiyar Barcelona, Xavi Hernandez ya fito ya yi magana game da wasu batutuwa da su ka shafi tsohuwar kungiyar da ya dade ya na yi wa bauta.

Xavi Hernandez ya bayyana lokacin da ya ke tunanin Lionel Messi zai yi ritaya daga kwallo a Duniya.

Xavi ya yi wasa da Lionel Messi na tsawon lokaci har zuwa kakar shekarar 2014.

A cewar Xavi, Lionel Messi zai iya cigaba da taka leda har zuwa lokacin da ya dumfari shekara 40. A halin yanzu tauraron mai shekara 32 da haihuwa ya lashe kofin Ballon D’or sau shida.

“Har yanzu ya na da shekaru kamar biyar ko bakwai masu kyau a gabansa.” Xavi ya ke cewa game da Messi lokacin da ya ke hira da wani tsohon ‘dan wasan Barcelona, Samuel Eto’o.

KU KARANTA: Tsohon kyaftin din Najeriya ya zo gida ya tallafawa mutane da abinci

Xavi ya yi hira ne da Samuel Eto’o a shafin Instagram kamar yadda mu ka samu labari daga Goal.com. “Ya na kula da jikinsa da kyau, Zai cigaba da buga kwallo har ya na 37, 38, 39.”

Tsohon ‘dan wasan tsakiyan ya ce babu shakka Messi zai buga wasan cin kofin Duniya na shekarar 2022 da za ayi a Qatar. Xavi zai so ace ya horar da Messi idan ya kai wannan lokaci.

Kocin na Al Sadd ya ce ya na da burin ya dawo kungiyar Barcelona a matsayin mai horas da ‘yan wasa nan gaba. Babu mamaki zai so ace har zuwa wannan lokaci Messi bai yi ritaya ba.

“A watan Junairu na yi magana da Darektan wasannin Barcelona (Eric Abidal) da Oscar Grau game da karbar aikin koci, amma lokacin bai zo mani a daidai ba. Ina bukatar kara gogewa”

Barcelona ta so Xavi ya canji Ernesto Valverde, amma a karshe aka maye gurbinsa da Quique Setien. Xavi ya bayyana cewa zai so ganin 'dan wasa Neymar lokacin da zai rike Barcelona.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel