Gwamnatin jihar Kano ta bude kamfanin Tiamin – Inji Alkalin Kotu

Gwamnatin jihar Kano ta bude kamfanin Tiamin – Inji Alkalin Kotu

A ranar Litinin, 4 ga watan Mayu, wata babban kotun tarayya da ke zama a garin Abuja ta bada umarnin cewa gwamnatin jihar Kano ta bude kamfanin casar shinkafar nan na Tiamin.

A watan Afrilun ne gwamnatin Kano ta garkame kamfanin casar shinkafar da sunan cewa ya yi kusa da dakin da aka killace masu COVID-19, wanda hakan ya na da illa ga lafiyarsu.

Alkali mai shari’a Okon Abang ya ba kamfanin gaskiya a wannan shari’a da aka yi jiya. Kamfanin na Tiamin Rice Producing Company ne ya kai gwamnatin Kano da jami’an tsaro kotu.

Daga cikin wadanda kamfanin ya kai gaban alkali sun hada da kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano da kuma ma’aikatan tsaro na NSCDC. A karshe kuma kamfanin ya samu nasara a kotu.

Lauyoyin Tiamin sun kalubalanci matakin da hukuma ta dauka na rufe kamfanin saboda kusanci da marasa lafiya. Lauyoyin sun gabatarwa kotu da tarin hujjojinsu a zaman da aka yi.

KU KARANTA: Coronavirus: Masu boye gaskiyar lafiyarsu za su shiga kotu da Gwamnati

Daga cikin hujjojin da lauyoyin kamfanin su ka bada shi ne su na cikin wadanda gwamnatin jihar Kano ta ba damar cigaba da aiki domin a samar da abinci a lokacin wannan annoba.

Saboda ganin yadda kamfanin ke taimakawa wajen nemawa jama’a abin yi da samar da isasshen abinci a Kano, lauyoyin kamfanin su ka nemi alkali ya ruguza matakin da aka dauka.

Alkali Abang ya jira wadanda ake tuhuma domin su zo gaban kotu su kare kansu, amma ba su yi hakan ba. Lauyoyin gwamnati da jami’an tsaron ba su iya zuwa kotu ba inji Daily Trust.

A karshe kotu ta amince da bukatun Tiamin, ta ce a bude kamfanin shinkafar, ta ce lallai an ba wannan kamfanin damar aikin casar shinkafa domin taimakawa Bayin Allah da abinci.

Babban kotun tarayyar ta yanke hukunci cewa rufe kamfanin ya ci karo da hakkin jama’a da dokar Najeriya ta tanada.

An bukaci IGP da kwamishinan ‘yan sanda su bude kamfanin.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel