4 a cikin 'yan Najeriya 10 su na fama da talauci - Kididdigar NBS ta nuna karuwar talauci da kaso 40

4 a cikin 'yan Najeriya 10 su na fama da talauci - Kididdigar NBS ta nuna karuwar talauci da kaso 40

- NBS, hukumar kididdiga ta gwamnatin tarayya, ta wallafa rahoton alkaluman talauci a Najeriya na shekarar 2019

- A cewar rahoton NBS, kaso 40.1 na jimillar 'yan Najeriya su na fama da talauci, hakan na nufin cewa fiye da 'yan Najeriya miliyan 82.9 talakawa ne

- Jihohi uku ma su karancin talauci a Najeriya sune; Lagos da kaso 4.5%, Delta da kaso 6.0% da jihar Osun mai kaso 8.5%

Hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ta wallafa rahoton alkaluman talauci a Najeriya na shekarar 2019.

A cikin rahoton da NBS ta saki ranar Litinin, 04 ga wata, ta ce akwai talakawa hudu a duk cikin mutane 10 a Najeriya.

Rahoton NBS ya nuna cewa kaso 40.1 na jimillar 'yan Najeriya su na fama da talauci. Hakan na nufin cewa fiye da 'yan Najeriya miliyan 82.9 talakawa ne a sikelin auna talauci a cikin kasa.

A cikin rahotonta na taba ka lashe da ta fitar, NBS ta ce mutane 4 a cikin 'yan Najeriya 10 su na samun kudin shiga da yawansu ya gaza N137,430 (kwatankwacin $353) a shekara.

4 a cikin 'yan Najeriya 10 su na fama da talauci - Kididdigar NBS ta nuna karuwar talauci da kaso 40

Makarantar 'ya'yan talakawa
Source: Twitter

NBS ta ce za ta fitar da cikkaken rahoto a kan talauci a Najeriya nan gaba kadan.

Hukumar ta bayyana cewa ta ware jihar Borno, mai fama da rikicin Boko Haram, daga cikin alkaluman talauci a Najeriya, na shekarar 2019, da ta fitar.

DUBA WANNAN: Annobar covid-19 ta hallaka mai juna biyu da mijinta ya shafa mata cutar a jihar Jigawa

A cewar NBS, ta ware Borno ne saboda rashin samun shiga cikin wasu yankunan jihar yayin tattara bayanai da alkaluma.

Jihohi uku da ke sahun gaba a yawan talakawa a Najeriya sune; Sokoto da kaso 87.73%, Taraba da kaso 87.72 da Jigawa mai kaso 87.02.

Jihohi uku ma su karancin talauci a Najeriya sune; Lagos da kaso 4.5%, Delta da kaso 6.0% da jihar Osun mai kaso 8.5%.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel