Likitoci sun gargadi yan Najeriya game da yin biris da dokokin Coronavirus

Likitoci sun gargadi yan Najeriya game da yin biris da dokokin Coronavirus

Yayin da aka sassauta dokar hana fita a jahohin Legas, Ogun da birnin tarayya Abuja, likitoci sun gargadi yan Najeriya game da hadarin dake tattare da yin fatali da dokokin kare kai.

Likitocin a karkashin kudin Association of Resident Doctors, ARD, sun bayyana cewa gwamnati za ta kara garkame mutane idan har aka samu yaduwar cutar Coronavirus a wannan lokaci.

KU KARANTA: Ji ka karu: Matakai 6 da ake bukata a dauka ga wanda ya yi mu’amala da mai cutar COVID19

Dakta Lanre Olosunde na asibitin koyarwa na jami’ar Ilorin ne ya bayyana haka yayin da yake tattaunawa da kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN a ranar Litinin.

Lanre ya koka kan sassauta dokar a wannan lokaci da ake samun hauhawan adadin masu cutar COVID19, inda ya nemi yan Najeriya su dabbaka dokokin kare kai don kiyaye yaduwarta.

Likitoci sun gargadi yan Najeriya game da yin biris da dokokin Coronavirus
Likitoci sun gargadi yan Najeriya game da yin biris da dokokin Coronavirus Hoto: Sunnewsonline
Asali: Facebook

“Kowa ya zauna cikin shirin sake komawa zaman gida idan har aka cigaba da samun ruruwar cutar a tsakanin mutane. Ina ganin bai dace a janye dokar a yanzu ba saboda akwai hujjojin dake nuna cutar na yaduwa a cikin jama’a.

“Kuma har yanzu bamu da isassun kayan gwaji, ina fata ba zamu taba kamo kasashen Amurka da Italiya wajen yawan mace mace ba, don haka nake kira ga jama’a su bi umarnin da likitoci suka fada musu.” Inji shi.

Likitan ya ja kunnen tsofaffi dake fama da cututtuka irin su cutar siga, sida, asma, kansa,cutar daji da sauransu dasu kula da kansu sosai a wannan lokaci saboda cutar ta fi kama su.

A makon da ta gabata ne shugaban kasa Buhari ya sanar da janye dokar ta bacin daya sanya a jahohin Legas, Ogun da babban birnin tarayya Abuja daga ranar Litinin 4 ga watan Mayu.

Sai dai Buhari ya sanya dokar hana fita daga karfe 8 na dare zuwa 6 na safiya, sa’annan ya tilasta ma jama’a sanya takunkumin fuska da kuma dakatar da tafiye tafiye tsakanin jahohi.

A wani labarin kuma, yan jam’iyyar PDP a majalisar wakilai sun yi kira ga shugaban kasa Muhammadu ya kara wa’adin dokar ta baci a jahohin Legas, Ogun da Abuja tsawon mako biyu.

Daily Trust ta ruwaito a ranar Litinin, 4 ga watan Mayu ne wa’adin dokar ta bacin da Buhari ya sanya a jahohin uku ya kare, don haka ake sa ran jama’a za su fara fita harkokinsu.

Buhari ya sanya dokar ne don yaki da yaduwar cutar Coronavirus a jahohin duba da cewa su suka fi yawan mutanen da suka kamu da cutar, da kuma wadanda suka mutu daga cutar.

Amma cikin wata sanarwa da yan PDP suka fitar, sun bayyana janye dokar a matsayin abin Allah wadai saboda zai kara ta’azzara yaduwar cutar a tsakanin jama’a fiye da kima.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel