COVID-19: Za a kai wadanda su ka yi rufa-rufa kotu a Kaduna – Kwamishina

COVID-19: Za a kai wadanda su ka yi rufa-rufa kotu a Kaduna – Kwamishina

- Za a fara kama duk wadanda su ka yi karya game da lafiyar jikinsu a Kaduna

- Wasu su na boyewa Malaman asibiti halin da su ke ciki ko inda su ka ziyarta

Gwamnatin jihar Kaduna ta yi gargadi cewa duk wanda aka samu ya na boye wani abu game da lafiyarsa ko a kan masu dauke da cutar COVID-19 zai gamu da fushin hukuma a gaban kotu.

Kwamishinar yada labarai ta jihar Kaduna, Dr. Amina Mohammed-Baloni ta shaidawa ‘yan jarida wannan, tare da bayyana irin nasarorin da gwamnatin Kaduna ta cin ma a wajen yaki da cutar.

Amina Mohammed-Baloni ta ce sun iya gano har 95% na wadanda su ka samu alaka da masu dauke da COVID-19 a jihar Kaduna. Kwamishinar ta ce sun gano mutane 28 da ke da cutar.

Dr. Baloni ta ce daya daga cikin wadanda su ka mutu a sanadiyyar cutar wani tsohon ma’aikacin gwamnati ne wanda ya boyewa likitoci cewa ya ziyarci jihar Kano a ‘yan kwanakin nan.

KU KARANTA: COVID-19: Za a dauki nauyin iyalin Likitocin da su ka mutu a Kaduna

“A sakamakon haka aka kwantar da shi a dakin killace marasa lafiya da sunan ya na fama da cutar numfashi. A nan ya mutu kafin a fito da sakamakon gwajin COVID-19 da aka yi masa."

Saboda masu yin irin wannan karya, kwamishinar lafiyar ta ce gwamnatin Kaduna za ta rika gurfanar da duk wanda aka samu ya yi wa ma’aikatan asibiti karya game da halin lafiyarsa.

Wannan Bawan Allah ya kai ziyara zuwa Kano a cikin kwanakin nan. Amma da aka je asibiti, sai ya nuna cewa sam ba haka ba. A karshe cutar ta kashe shi kafin malaman asibitin su farga.

Jihar Kano mai makwabtaka da Kaduna ta na cikin inda cutar ta yi kamari a halin yanzu a Najeriya. Mafi yawan almajiran da ke dauke da COVID-19 a Kaduna sun dawo ne daga Kano.

Kawo yanzu Dr. Amina Baloni ba ta bayyana laifin da za a kama wadanda su ka boye gaskiyar lamarin lafiyarsu ba. Gwamnatin Kaduna ta na ta kokarin ganin bayan wannan annoba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng