Covid-19: Gwamnatin Katsina ta rufe wasu manyan kasuwanni uku a jihar

Covid-19: Gwamnatin Katsina ta rufe wasu manyan kasuwanni uku a jihar

Gwamnatin Katsina ta bayar da umarnin sake rufe wasu manyan kasuwanni uku da ke ci sati - sati a jihar.

Sakataren gwamnatin jihar Katsina, Mustapha Inuwa, ne ya sanar da hakan a cikin wani jawabi da ya fitar ranar Lahadi, 03 ga watan Mayu.

Kasuwanni da wannan umarni ya shafa sune; Garkin Daura, Dutsi, da Kayawa.

An rufe kasuwannin ne bayan gwamnati da ma su ruwa da tsaki sun nuna damuwarsu a kan hauhawar mutanen da ke kamuwa da cutar covid-19 a jihar Katsina.

A cewar Inuwa, umarnin rufe kasuwannin ya fara aiki nan take. Ya ce rufe kasuwannin na daga cikin matakan dakile yaduwar annobar covid-19 a jihar Katsina.

Ya bukaci mazauna jihar su kasance ma su biyayya ga doka, tare da bayyana cewa gwamnati ta bawa jami'an tsaro umarnin tabbatar da biyayya ga umarnin rufe kasuwannin.

Kimanin sati biyu da suka gabata, gwamnatin jihar Katsina ta sanar da rufe karamar hukumar Daura biyo bayan mutuwar wani mai dauke da kwayar cutar covid-19.

Covid-19: Gwamnatin Katsina ta rufe wasu manyan kasuwanni uku a jihar
Gwamnan Katsina; Aminu Bello Masari
Asali: UGC

A wani labari da jaridar Daily Trust ta wallafa a yau, Litinin, 04 ga watan Mayu, ta bayyana cewa an rufe fadar masarautar Daura bayan samun bullar annobar covid-19.

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, dan asalin karamar hukumar Daura ne.

Sakataren gwamnatin jihar Katsina, Dakta Mustapha Inuwa, ya tabbatar da rufe fadar sarkin tare da bayyana cewa sakamakon gwajin da ake jira ne kadai zai nuna lokacin da za a bude fadar.

DUBA WANNAN: Bayanai sun fito a kan musabbabin mutuwar babban sarki a Zamfara

"Ba wani sabon abu bane, haka tsarin ya ke duk duniya, matukar an samu mai dauke da kwayar cutar covid-19. An rufe fadar yayin da aka dauki jinin mutane zuwa cibiyar gwaji," a cewarsa.

Da ya ke magana a kan lamarin, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isa, ya ce, "mu dama a wurin rundunar 'yan sanda, karamar hukumar Daura a rufe ta ke, hakan kuma ya shafi kowanne lungu da sako da kuma kowanne gida.

"Aikin rundunar 'yan sanda shine tabbatar da dokar gwamnati a kan dukkan jama'a."

A ranar 17 ga watan Afrilu ne uwargidan sarkin Daura, Hajiya Binta Umar, ta mutu bayan ta sha fama da wata doguwar jinya. Ta mutu ta na da shekaru 70 a duniya.

An tabbatar da samun karin mutane 8 da su ka kamu da kwayar cutar covid-19 a ranar Lahadi, kamar yadda cibiyar yaki da cututtuka ma su yaduwa a kasa (NCDC) ta sanar.

Yanzu haka akwai jimillar mutane 46 da aka tabbatar da cewa su na dauke da kwayar cutar covid-19 a jihar Katsina.

A yayin da aka sallami mutane 6 da su ka warke daga cutar covid-19 a Katsina, cutar ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 7.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng