Yadda aka cakuda Zamfarawa 40 a cikin shanu aka shigar da su Legas (Bidiyo, Hoto)

Yadda aka cakuda Zamfarawa 40 a cikin shanu aka shigar da su Legas (Bidiyo, Hoto)

Jami'an tsaro a Legas sun datse wata babbar motar daukan kaya da aka cakuda mutane a cikin shanu domin shigar da su cikin jihar, kamar yadda jaridar Vanguard ta rawaito.

Babbar motar, wacce ta taso daga jihar Zamfara, an datseta ne a daidai 'Berger' da ke kan babban titin Lagos zuwa Ibadan.

Yanzu haka jami'an gwamnatin jihar Legas sun umarci babbar motar, da duk abin da ke cikinta, ta koma jihar da ta fito.

Yadda aka cakuda Zamfarawa 40 a cikin shanu aka shigar da su Legas (Bidiyo, Hoto)

Yadda aka cakuda Zamfarawa 40 a cikin shanu aka shigar da su Legas
Source: UGC

Yadda aka cakuda Zamfarawa 40 a cikin shanu aka shigar da su Legas (Bidiyo, Hoto)

Zamfarawa 40 da aka kai Legas a cakude cikin shanu
Source: UGC

A ranar Alhamis, 30 ga watan Afrilu, Legit.ng ta wallafa labarin cewa an kama wasu manyan motocin dako guda biyu da aka boye mutane a cikinsu a yayin da suke kokarin shiga jihar Kaduna ta kan iyakarta da jihar Kano.

An cakuda mutane da dabbobi domin yin basaja wajen shigar da su jihar Kaduna.

Wannan ba shine karo na farko da aka samu mutane a boye a cikin manyan motocin dako suna kokarin shiga jihar Kaduna daga Kano ba.

A cikin sanarwar da kwamishinan harkokin cikin gida a jihar Kaduna ya fitar, ya bayyana cewa, "mun samu labarin cewa wasu manyan motocin dako sun shigo har Gwargwaji a Zariya, jihar Kaduna, daga Kano.

DUBA WANNAN: Bayanai sun fito a kan musabbabin mutuwar babban sarki a Zamfara

"Mun yi nasarar cafkesu a yankin karamar hukumar Zariya a yunkurinsu na son shigowa jihar Kaduna.

"An yi hikima da wayon boye mutane a cikin dabbobi, wasu tarkacen kaya da baburan hawa. Amma duk da haka mun yi nasarar ganosu, kuma mun tursasu komawa inda suka fito, kamar yadda dokar jihar Kaduna ta tanada.

"Jami'anmu na aikin tabbatar da dokokin jiha a kan iyakokinmu, kuma suna kama fasinjoji tare da rakasu kan iyakar jihar da suka fito."

Hana shiga jihar Kaduna na daga cikin matakan da gwamnatin jihar ta dauka domin dakile yaduwar annobar covid-19.

A ranar Talata ne Legit.ng ta wallafa labarin cewa jami'an tsaro tare da hadin gwuiwar jami'an gwamnatin Kaduna sun kama wasu manyan motocin dakon kayan abinci da aka boye mutane a cikinsu.

An kama motocin ne a kauyen Sabon Gida da ke yankin karamar hukumar Ikara yayin da suke kokarin shiga jihar Kaduna.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel