Covid-19: Ta harbi mutane 66 a Sokoto, Tambuwal ya rufe jihar, ya nemi tallafin FG

Covid-19: Ta harbi mutane 66 a Sokoto, Tambuwal ya rufe jihar, ya nemi tallafin FG

Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya ce a halin yanzu jihar ta rasa rayuka takwas sannan mutum 66 sun kamu da cutar coronavirus.

Tambuwal, wanda ya sanar da hakan ga manema labarai, yace kiyasin nan yana tura jihar Sokoto a kan gaba wajen yaduwar annobar a Najeriya.

"Duk da rashin dadin kiyasin, kwamitin yaki da cutar coronavirus ta jihar na kokarin shawo kan wannan kalubalen," in ji shi.

"Sakamakon yawaitar masu cutar a jihar, ina kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da kwamitin yaki da cutar na kasa da su kawo taimakon gaggawa ta hanyar samar da kayan aiki ga jihar nan," in ji gwamnan.

Covid-19: Ta harbi mutane 66 a Sokoto, Tambuwal ya rufe jihar, ya nemi tallafin FG

Covid-19: Ta harbi mutane 66 a Sokoto, Tambuwal ya rufe jihar, ya nemi tallafin FG
Source: UGC

Hukumar kula da cutuka masu yaduwa ta NCDC ta sanar da cewa mutum 170 sun kara kamuwa da cutar COVID-19 a fadin Najeriya. Hakan ne ya kai jimillar masu cutar zuwa 2558 inda maza suka fi yawa a ciki.

"A yayin da wannan kalubalen ke ci gaba da yawaita tare da tada hankali, gwamnatin tarayya da na jihar na kokarin shawo kan shi don gujewa yaduwar annobar.

"Babban matakin da gwamnatin tarayya ta dauka shine haramta shige da fice tsakanin jihohi wanda ke kawo rufewar iyakokin jihohi.

"Tabbatar da dokar saka takunkumin fuska na dole yana daga cikin matakan," a cewarsa.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta bayyana, gwamnan ya saka dokar ta baci a jihar wanda zai fara daga ranar 4 Mayun 2020, daga karfe 8 na yamma zuwa 6 na safe na kowacce rana.

KU KARANTA KUMA: COVID-19: Kano na cikin mawuyacin hali - Ganduje

Kamar yadda gwamnan ya bayyana, "Wannan dokar ba ta taba jami'ai masu ayyukan da ake bukata ko yaushe ba.

"Hakazalika, dukkan ma'aikatan gwamnati da ke mataki na 13 zuwa sama dole ne su saka takunkumin fuska kafin su je aiki."

A wani labarin kuma, mun ji cewa kimanin sati biyu da suka gabata, gwamnatin jihar Katsina ta sanar da rufe karamar hukumar Daura biyo bayan mutuwar wani mai dauke da kwayar cutar covid-19.

A wani labari da jaridar Daily Trust ta wallafa a yau, Litinin, 04 ga watan Mayu, ta bayyana cewa an rufe fadar masarautar Daura bayan samun bullar annobar covid-19.

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, dan asalin karamar hukumar Daura ne.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel