Da duminsa: EFCC za ta gurfanar da tsohon ministan Jonathan

Da duminsa: EFCC za ta gurfanar da tsohon ministan Jonathan

Hukumar yaki da rashawa da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC, ta shirya gurfanar da babban lauyan Najeriya kuma tsohon ministan ayyukan na musamman, Kabiru Turaki.

EFCC za ta gurfanar da shi ne a gaban wata babbar kotun tarayya da ke Abuja a yau Litinin.

Mukaddashin jami'in yada labarai na hukumar, Tony Orilade, ya ce gurfanarwar ta biyo bayan zarginsa da ake da laifuka 16.

Zai gurfana ne a gaban Mai shari'a Inyang Ekwo.

Da duminsa: EFCC za ta gurfanar da tsohon ministan Jonathan

Da duminsa: EFCC za ta gurfanar da tsohon ministan Jonathan
Source: UGC

Turaki ya jagoranci ma'aikatar al'amura na musamman tsakanin 2013 zuwa 2015 sannan ya lura da ma'aikatar kwadago daga 2014 zuwa 2015 a karkashin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.

Kamar yadda jaridar The Punch ta bayyana, babban lauyan na hannu dama ne a wurin tsohon dan takarar kujerar shugaban kasa na shekarar 2019 karkashin jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar.

Shine na biyu a kungiyar lauyoyin Atiku Abubakar wadanda suka kalubalanci nasarar shugaban kasa Muhammadu Buhari a kotu a zaben da ya gabata.

KU KARANTA KUMA: COVID-19: Kano na cikin mawuyacin hali - Ganduje

Sauran wadanda EFCc za ta gurfanar tare da tsohon ministan sune: Sampson Okpetu, tsohon mataimakinsa na musamman, Samtee Essentials Limited da Pasco Investment Limited, wadanda duk aka gano kamfanonin Okpetu ne.

A wani labari na daban, Jam’iyyar APC mai mulki ta karbi shawarwarin da tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya ba shugaban kasa Muhammadu Buhari na fadada tattalin arziki.

Sai dai duk da amincewa da wadannan shawarwari, jam’iyyar APC ta zargi Atiku Abubakar da kin dabbaka manufofin da ya ke ambata a yau, a lokacin da ya ke cikin gwamnatin PDP.

APC ta ce Atiku Abubakar wanda ya shafe shekaru takwas a matsayin mataimakin shugaba Olusegun Obasanjo bai yi kokarin kawo gyare-gyaren da yanzu ya ke fitowa ya na fada ba.

Jam’iyyar APC ta yi wannan jawabi ne ta bakin sakataren yada labarai, Mallam Lanre Issa-Onilu a ranar 2 ga watan Mayu, 2020. APC ta fitar da jawabin ne a babban birnin tarayya Abuja.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel