Kwamishinan Bauchi ya bayyana ainahin maganin da suka yi amfani da shi wajen warkar da masu COVID-19 a jahar

Kwamishinan Bauchi ya bayyana ainahin maganin da suka yi amfani da shi wajen warkar da masu COVID-19 a jahar

Maganin zazzabin cizon sauro mai suna Chloroquine, ya taimaka wajen warkar da masu coronavirus a jahar Bauchi.

Kwamishinan lafiya na jahar, Dr. Aliyu Maigoro, ya ce harda Gwamna Bala Mohammed cikin wadanda maganin ya warkar.

Maigoro, wanda ya goyi bayan matsayar gwamnan kan maganin chloroquine, ya yi jawabi ga manema labarai a jiya Lahadi, ta wayar salula.

Kwamishinan Bauchi ya bayyana ainahin maganin da suka yi amfani da shi wajen warkar da masu COVID-19 a jahar

Kwamishinan Bauchi ya bayyana ainahin maganin da suka yi amfani da shi wajen warkar da masu COVID-19 a jahar
Source: Twitter

Ya ce maganin zazzabin cizon sauron shine abun da aka bai wa marasa lafiya biyar da aka sallama kimanin makonni biyu da suka gabata bayan gwamnan ya warke.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa marasa lafiya shida sun warke kuma an sallame su tun bayan barkewar annobar.

Maigoro ya ce: “Kamar yadda gwamnan ya fada daidai a jawabinsa, wannan magani na chloroquine shine aka yi amfani da shi wajen warkar da wasu marasa lafiya biyar wadanda aka sallama bayan gwamnan ya warke.”

KU KARANTA KUMA: Ji ka karu: Matakai 6 da ake bukata a dauka ga wanda ya yi mu’amala da mai cutar COVID19

A wani labarin, mun ji cewa ma’aikatan lafiya biyar aka tabbatar cewa sun kamu da muguwar cutar nan ta COVID-19 a jihar Bauchi. Bayan haka kuma an gano wasu almajirai bakwai da ke dauke da wannan cuta.

Akalla yara bakwai ne daga cikin almajirai 38 da aka shigo da su Bauchi daga jihar Kano aka samu su na dauke da cutar COVID-19 inji kwamitin da ya ke yaki da COVID-19 a jihar Bauchi.

Shugaban hukumar da ke kula da matakin farko na kiwon lafiya a jihar Bauchi, Dr. Rilwanu Mohammed ya shaidawa Daily Trust wannan a lokacin jaridar ta tuntubesa a wayar salula.

Rilwanu Mohammed wanda ya na cikin kwamitin yaki da cutar COVID-19 a Bauchi ya bayyana cewa jihar ta samu karin wasu mutane 19 masu Coronavirus a cikin karshen makon nan.

Dr. Mohammed ya fadawa jaridar Daily Trust cewa daga cikin wadanda su ka kamu da wannan cuta har da 'dan shekara hudu wanda ya hadu da wani mutumi da ya dawo daga Legas.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel