Da Atiku Abubakar aka ci gwamnatin Shugaba Obasanjo maras hangen nesa - APC

Da Atiku Abubakar aka ci gwamnatin Shugaba Obasanjo maras hangen nesa - APC

Jam’iyyar APC mai mulki ta karbi shawarwarin da tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya ba shugaban kasa Muhammadu Buhari na fadada tattalin arziki.

Sai dai duk da amincewa da wadannan shawarwari, jam’iyyar APC ta zargi Atiku Abubakar da kin dabbaka manufofin da ya ke ambata a yau, a lokacin da ya ke cikin gwamnatin PDP.

APC ta ce Atiku Abubakar wanda ya shafe shekaru takwas a matsayin mataimakin shugaba Olusegun Obasanjo bai yi kokarin kawo gyare-gyaren da yanzu ya ke fitowa ya na fada ba.

Jam’iyyar APC ta yi wannan jawabi ne ta bakin sakataren yada labarai, Mallam Lanre Issa-Onilu a ranar 2 ga watan Mayu, 2020. APC ta fitar da jawabin ne a babban birnin tarayya Abuja.

Mallam Lanre Issa-Onilu ya ce jam’iyyar APC ta yaba da kokarin da Alhaji Atiku Abubakar ya yi na ba shugaban kasa Muhammadu Buhari shawarar yadda za a fadada tattalin arzikin kasa.

Lanre Issa-Onilu ya ce amma APC ta yi mamakin yadda Atiku Abubakar ya ki fitowa ya yabawa kokarin da gwamnatin Buhari ta ke ta yi a shekarun nan na fadada tattalin arzikin kasar.

KU KARANTA: COVID-19: Atiku ya fadi yadda za a ragewa mutane radadi a Najeriya

Atiku ya rubuta wata takarda ne da ya yi wa taken ‘Yadda za a ceto Najeriya daga rami’ inda ya yi magana game da abin da ya kamata gwamnati ta yi bayan karyewar farashin mai.

APC ta ce a wancan lokaci Atiku ya samu damar fadada tattalin arzikin Najeriya ta yadda gwamnatin za ta rage dogara da arzikin danyen mai kamar yadda ya ke bada shawara.

“Atiku Abubakar ya yi shekaru takwas a kujera mai karfi ta mataimakin shugaban kasa kuma shugaban majalisar saida kadarorin gwamnati inda ya samu dama.” Inji Issa-Onilu.

Da ta ke martani a kan wannan takarda, jam’iyyar APC ta ce: “Tun 2016, gwamnatin Buhari ta kama hanyar fadada tattalin Najeriya musamman a bangaren noma inda ta fi wayau.”

“A sakamakon haka yanzu duk Afrika babu kasar da ta kai Najeriya noma shinkafa. Yanzu ana samun ton miliyan bakwai na shinkafa duk shekara a Najeriya.” Inji jam’iyyar APC.

“Haka kuma a samakon kokarin gwamnatin da Buhari ya ke jagoranta na inganta noma, an samu nasarar hada takin zamani a gida. Ko ‘yan adawan shugaba Buhari sun san wannan.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel