Kano: Mun horas da Ma’aikatan gwaji, mun wayar da kan mutane a makon jiya - NCDC

Kano: Mun horas da Ma’aikatan gwaji, mun wayar da kan mutane a makon jiya - NCDC

- Bayan Shugaban kasa Buhari ya bukaci a kai wa Jihar Kano agaji kwanaki

- Hukumar NCDC ta bude dakunan gwaji uku domin yakar cutar Coronavirus

- Ana kuma wayar da kan jama’a tare da horas da Malaman asibiti kan cutar

Bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi alkawarin taimakawa jihar Kano da duk wani agajin da ake bukata na yaki da annobar COVID-19, hukumar NCDC ta tashi tsaye a jihar.

A cikin makon da ya gabata Legit.ng Hausa ta samu labarin cewa an fadada yawan dakunan da ake yin binciken kwayar cutar COVID-19 a jihar Kano domin gano masu dauke da cutar.

A ranar Lahadi, 3 ga watan Mayu, 2020, hukumar NCDC ta bayyana cewa an kaddamar da wani sabon dakin gwajin COVID-19. Wannan shi ne dakin gwaji na uku da aka gina a Kano.

Idan ba ku manta ba kwanaki har ta kai an rufe dakin da ake yin gwajin COVID-19. Yanzu an samu dakuna da-dama da ake daukar danshin hancin marasa lafiya domin yi masu gwaji.

KU KARANTA: Dangote ya gina dakin gwajin kwayar cutar COVID-19 a Kano

Shugaban hukumar NCDC, Chikwe Ihekweazu ya samu halartar taron kaddamar da dakin gwajin da gwamnatin jihar Kano ta yi. Gidauniyar Aliko Dangote ta dauki nauyin wannan aiki.

Bayan fadada yawan wuraren gwaji a cikin makon da ya gabata, hukumar NCDC ta kuma bayyana cewa ta yi wa malaman asibiti horo domin su koyi yadda ake yin gwajin COVID-19.

Ma’aikatan NCDC sun horas da malaman lafiya a asibitin koyon aiki na Malam Aminu Kano da kuma jami’ar Bayero da ke jihar. Wannan duk ya na cikin irin kokarin gwamnatin tarayya.

Ma’aikatan NCDC sun rika yawo lungu-lungu a jihar Kano su na yunkurin wayar da kan jama’a game da hadarin wannan mummunar annoba. NCDC ta bayyana wannan a shafin Tuwita.

Jami’an na NCDC sun kuma fadakar da jama’a game da yadda za su rika bankado wadanda ake zargin su na dauke da kwayar cutar COVID-19. Hukumar duk ta yi wannan ne a makon jiya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel