Korona ta harbi sabbin mutane 170 a Najeriya, Kano, Bauchi da Kaduna su na sahun gaba a wannan karon

Korona ta harbi sabbin mutane 170 a Najeriya, Kano, Bauchi da Kaduna su na sahun gaba a wannan karon

Hukumar yaki da cututtuka ma su yaduwa a kasa (NCDC) ta ce annobar cutar covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 170 a fadin Najeriya.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da NCDC ta fitar da misalin karfe 12:01 na safiyar ranar Litinin, 04 ga watan Mayu, 2020.

A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na tuwita, ta sanar da cewa karin sabbin mutane 170 din sun fito daga jihohin Najeriya kamar haka;

39-Lagos

29-Kano

24-Ogun

18-Bauchi

15-Kaduna

12-FCT

12-Sokoto

8-Katsina

7-Borno

3-Nasarawa

2-Adamawa

1-Oyo

NCDC ta ce ya zuwa karfe 11:50 na daren ranar Lahadi, 03 ga watan Mayu, akwai jimillar mutane 2558 da aka tabbatar da cewa suna dauke da kwayar cutar covid-19 a Najeriya.

An sallami mutane 400 bayan an tabbatar da samun saukinsu, a yayin da cutar ta hallaka jimillar mutane 87.

Alkaluman NCDC na ranar Lahadi, 03 ga watan Afrilu, sun nuna cewa an samu raguwar mutanen da annobar ta harba idan aka kwatanta da alkaluman baya bayan nan da hukumar ta fitar.

Kazalika, alkaluman sun nuna cewa annobar ta na kara mamaya a jihohin arewacin Najeriya.

DUBA WANNAN: Covid-19: Sakamakon gwajin hadiman Buhari da su ka halarci jana'izar Abba Kyari ya fito

Cutar coronavirus ta kashe dan majalisar jihar Nasarawa, Adamu Sulaiman, kamar yadda gidan talabijin na Channels ya rawaito.

Sulaiman ne majinyaci na farko da ya rasu sakamakon cutar covid-19 a Nasarawa tun bayan da aka gano annobar ta shiga jihar.

Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya sanar da mutuwar dan majalisar a yayin da yake jawabi ga manema labarai a garin Lafia, babban birnin jiha.

Da safiyar ranar Lahadi ne Legit.ng ta wallafa labarin mutuwar Sarkin masarautar Kauran Namoda a jihar Zamfara, Alhaji Muhammad Ahmad Asha.

Jaridar The Punch ta wallafa cewa sakataren yada labarai na kwamitin yaki da cutar covid-19 a jihar Zamfara, Mustafa Jafaru, ya ce basaraken ya na killace ne a asibitin kwararru da ke garin Gusau, babban birnin jiha.

Jafaru ya bayyana cewa an dauki jininsa tare da aika shi zuwa dakin gwaji da ke Abuja, amma har ya zuwa wannan lokaci ana dakon fitowar sakamakon gwajin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel