Wasu Likitoci da Almajirai sun kamu da cutar COVID-19 a jihar Bauchi

Wasu Likitoci da Almajirai sun kamu da cutar COVID-19 a jihar Bauchi

Ma’aikatan lafiya biyar aka tabbatar cewa sun kamu da muguwar cutar nan ta COVID-19 a jihar Bauchi. Bayan haka kuma an gano wasu almajirai bakwai da ke dauke da wannan cuta.

Akalla yara bakwai ne daga cikin almajirai 38 da aka shigo da su Bauchi daga jihar Kano aka samu su na dauke da cutar COVID-19 inji kwamitin da ya ke yaki da COVID-19 a jihar Bauchi.

Shugaban hukumar da ke kula da matakin farko na kiwon lafiya a jihar Bauchi, Dr. Rilwanu Mohammed ya shaidawa Daily Trust wannan a lokacin jaridar ta tuntubesa a wayar salula.

Rilwanu Mohammed wanda ya na cikin kwamitin yaki da cutar COVID-19 a Bauchi ya bayyana cewa jihar ta samu karin wasu mutane 19 masu Coronavirus a cikin karshen makon nan.

Dr. Mohammed ya fadawa jaridar Daily Trust cewa daga cikin wadanda su ka kamu da wannan cuta har da 'dan shekara hudu wanda ya hadu da wani mutumi da ya dawo daga Legas.

KU KARANTA: Har gobe wasu ba su yarda akwai COVID-19 ba - Gwamnatin Borno

Har ila yau, Mohammed ya bayyana cewa daga cikin malaman lafiyan da su ka kamu da wannan cuta akwai likitoci uku, da ungonzoma daya da kuma wani malamin wayar da kan jama’a.

Duka wadannan ma’aikatan lafiya sun kasance su na aiki a asibitocin jihar ne kafin su harbu da COVID-19. Rilwanu Mohammed ya ce yanzu an kwantar da dukkansu a asibiti ana jinya.

“A ranar Juma’a mun samu karin sababbin mutane tara da ke da COVID-19, a ranar Asabar kuma mu ka sake samun wasu mutane goma, wanda hakan ya sa masu cutar su ka kai 48.”

Dr. Mohammed ya kara da cewa: “Mutum shida sun warke, kuma an sallame su, babu wanda aka samu ya mutu a jihar Bauchi.” Likitan ya kuma bada tarihin sauran masu dauke da cutar.

"Daga cikin wasu mutane 78 da su ka dawo da Enugu da Fatakwal, an samu mutum uku da ke COVID-19." Gwamnatin Bauchi ta ce za ta dage wajen wayar da kan jama’a a kan cutar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit Nigeria

Online view pixel