Jihar Zamfara ba za ta rage albashin Ma’aikata ba – Gwamna Matawalle

Jihar Zamfara ba za ta rage albashin Ma’aikata ba – Gwamna Matawalle

Mai girma gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya shaidawa ma’aikata cewa su sha kuruminsu domin ba zai rage masu albashi kamar yadda wasu gwamnonin su ke yi ba.

Alhaji Bello Matawalle ya tabbatarwa ma’aikatan gwamnatin Zamfara cewa babu maganar zaftare masu albashi. Gwamnan ya ce za a cigaba da biyansu kudinsu kamar yadda aka saba.

Gwamnan ya yi wannan jawabi ne ta bakin Darekta-Janar na yada labaran jihar Zamfara, Yusuf Idris. Gwamnan ya ce duk da zaman gidan da ake yi, ma’aikata za su rika samun albashinsu.

Bayan haka gwamnatin Bello Matawalle ta amince da bashin Naira miliyan 470 da za a rabawa ma’aikata domin su saye kayan abinci a cikin sauki da rahusa a dalilin annobar Coronavirus.

Yusuf Idris ya yi kira ga ma’aikata su yaba da kokarin gwamnatin Matawalle na inganta rayuwa da walwala da jin dadinsu ta hanyar dagewa a bakin aiki a duk lokacin da su ka koma ofis.

KU KARANTA: Ekiti: Ma'aikata sun samu gibi a albashi saboda annobar COVID-19

Jihar Zamfara ba za ta rage albashin Ma’aikata ba – Gwamna Matawalle
Gwamna Matawalle ya ce babu maganar zaftarewa ma'aikatan Zamfara albashi
Asali: UGC

Rahotanni sun bayyana cewa gwamnan ya bayyana wannan albishir ne wajen buda bakin azumi da ya yi da shugabanin ma’aikatan gwamnatin jihar a gidan gwamnati a ranar Juma’ar nan.

Ma’aikatan jihar Zamfara sun ji dadin wannan mataki da gwamna Bello Matawalle ya dauka. A halin yanzu akwai jihohin da su ka zaftarewa ma’aikata albashi saboda halin da aka shiga.

Shugaban kungiyar kwadago na reshen jihar Zamfara, Bashir Mafara ya godewa mai girma gwamna Bello Matawalle a lokacin da ya yi jawabi a madadin ma’aikatan gwamnatin jihar.

Jaridar Punch ta ce Kwamred Mafara ya yabawa gwamnan na kin biyewa takwarorinsa da su ka rage albashin ma’aikata a sakamakon lalitarsu da ta yi kasa a wannan lokacin annoba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel