COVID-19 ta hallaka wasu masu jinya a Legas – Kwamishinan lafiya
- An kuma samun wadanda cutar COVID-19 ta ga karshensu a Najeriya
- Gwamnatin Jihar Legas ta bada sanarwar cewa mutum uku sun mutu
- Kwamishinan lafiyan Legas bai bada karin bayani game da mutuwar ba
Gwamnatin jihar Legas ta fito ta bayyana cewa an samu karin wasu Bayin Allah da su ka mutu a wajen jinyar cutar COVID-19 da ake ta fama da ita a wannan marra.
Kwamishinan lafiya na jihar Legas, Akin Abayomi ya bada sanarwar wannan mutuwa da aka yi a ranar Lahadi, 3 ga watan Mayu, 2020, kamar yadda mu ka samu rahoto.
Kwamishinan ya yi wannan bayani ne a shafinsa na sada zumunta na Tuwita kamar yadda ya saba. Sai dai kwamishinan bai bada wani karin bayani game da mutuwar ba.
Farfesa Akin Abayomi bai fito ya fadi yadda masu jinyar su ka mutu ba, haka zalika bai fadi asibitin da ake jinyarsu ba. Kuma ba a bayyana shekarun mamatan ba.
KU KARANTA: Yadda na ji a lokacin da COVID-19 ta kama ni – Mohammed Atiku
Da ya ke bada sanarwar, Farfesa Abayomi ya ce: “An samu sababbin mutane 62 da su ka kamu da cutar COVID-19 a Legas a zuwa ranar Asabar 2 ga watan Mayu, 2020.”
“Adadin masu dauke da COVID-19 a Legas sun kai mutane 1, 084.” Kwamishinan ya kara da cewa: “Mutane 22 sun samu sauki a cikin masu jinyar cutar COVID-19.”
Aboyami ya bayyana cewa maza 14 da mata 8 ne su ka warke daga cutar a jiya. “Wannan ya sa wadanda aka sallama daga cikin marasa lafiya ya tashi zuwa 247.”
A karshe Aboyami ya ce: “An samu karin mutane uku da su ka mutu a wajen fama da COVID-19, wannan ya sa adadin wadanda cutar ta kashe ya kai 28 a jihar Legas.”
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng