Cutar Coronavirus ce ta kashe dan majalisar dokokin jahar Nasarawa
- Rahoto ya kawo cewa cutar coronavirus ce ta kashe dan majalisar jihar Nasarawa, Adamu Sulaiman
- Dan majalisar ne majinyaci na farko da ya rasu sakamakon annobar a jihar Nasarawa tun bayan da aka gano cutar ta shiga jihar
- Gwamna Sule ya sanar da cewa Sulaiman ya rasu tun kafin sakamakon gwajinsa ya fito
Cutar coronavirus ta kashe dan majalisar jihar Nasarawa, Adamu Sulaiman, gidan talabijin na Channels ya ruwaito.
Sulaiman ne majinyaci na farko da ya rasu sakamakon annobar a jihar Nasarawa tun bayan da aka gano cutar ta shiga jihar.
Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya sanar da mutuwar dan majalisar a yayin da yake jawabi ga manema labarai a garin Lafia, babban birnin jihar.

Asali: UGC
A yayin sanar da inda aka kwana a kan cutar a jihar, Gwamna Sule ya sanar da cewa Sulaiman ya rasu tun kafin sakamakon gwajinsa ya fito.
Ya yi bayanin cewa, bayan an samu sakamakon gwajin dan majalisar, iyalansa da wadanda ke rayuwa tare dashi duk an killacesu.
Gwamnan ya kara da cewa, an mika samfur dinsu ga hukumar kula da cututtuka masu yaduwa ta NCDC.
KU KARANTA KUMA: Mace-macen Kano: Allah ya yi wa tsohon Jarman Kano rasuwa
Kafin rasuwarsa, Sulaiman ne dan majalisa mai wakiltar mazabar jihar Nasarawa ta tsakiya a jihar.
A wani labari mai kama da wannan, kun ji cewa Allah ya yi wa sarkin Rano ta jihar Kano, Alhaji Tafida Abubakar II rasuwa.
Sarkin wanda ake kira da Autan Bawo, ya rasu ne a ranar Asabar yana da shekaru 74 a duniya.
Turakin Rano kuma dan majalisar mai wakiltar Rano, Kibiya da Bunkure, Alhaji Alhassan Rurum ne ya tabbatar da wannan babban rashin ga jaridar Solacebase.
Kamar yadda ya bayyana, za a birne marigayin basaraken ne da yammacin ranar Asabar a masarautarsa.
Marigayin sarkin ya rasu ya bar yara 17 da kuma mata biyu. Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa an kwantar da Sarkin a asibiti a ranar Juma'a bayan rashin lafiyar da ya kwanta.
An gano cewa an hanzarta mika Sarkin asibitin koyarwa na Mallam Aminu Kano da ke birnin Kano.
A cikin halin tsanantar rashin lafiyar, an mayar da shi asibitin kwararrun da ke Nasarawa don ci gaba da samun kulawar masana kiwon lafiya.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng