Bayanai sun fito a kan musabbabin mutuwar babban sarki a Zamfara

Bayanai sun fito a kan musabbabin mutuwar babban sarki a Zamfara

Da safiyar ranar Lahadi ne Legit.ng ta wallafa labarin mutuwar Sarkin masarautar Kauran Namoda a jihar Zamfara, Alhaji Muhammad Ahmad Asha.

Sarkin ya rasu ne da safiyar ranar Lahadi, 3 ga watan Mayun 2020 bayan fama da gajeriyar rashin lafiya kamar yadda wani na kusa da fadar sarkin ya tabbatar wa BBC.

Ya rasu yana da shekaru 71 a duniya, ya kuma bar mata uku da yaya da dama.

A cewar jaridar The Punch, Sarkin ya mutu ne a asibitin da aka killace shi.

Jaridar ta ce ya ana zargin cewa cutar covid-19 ce ta yi sanadin mutuwarsa.

The Punch ta ce sakataren yada labarai na kwamitin yaki da cutar covid-19 a jihar Zamfara, Mustafa Jafaru, ya ce basaraken ya na killace ne a asibitin kwararru da ke garin Gusau, babban birnin jiha.

Jafaru ya bayyana cewa an dauki jininsa tare da aika shi zuwa dakin gwaji a Abuja, amma har ya zuwa wannan lokaci ana dakon fitowar sakamakon gwajin.

Bayanai sun fito a kan musabbabin mutuwar babban sarki a Zamfara

Bayanai sun fito a kan musabbabin mutuwar babban sarki a Zamfara
Source: UGC

Ya kara da cewa har yanzu gawar Sarkin ta na asibitin, yayin da ake jiran yi ma sa jana'iza.

DUBA WANNAN: 'A fusace na ke a lokacin' - Dattijon da aka kama saboda ya zagi Buhari ya yi bayani

Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Sani Yariman Bakura, ne ya nada marigayin a matsayin sarkin masarautar Kauran Namoda na 71 a shekarar 2004.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel