Buhari ya maye gurbin Mallam Mohammed Kari, ya nada sabon shugaban NAICOM

Buhari ya maye gurbin Mallam Mohammed Kari, ya nada sabon shugaban NAICOM

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya amince da nadin Mista Sunday Thomas a matsayin kwamishina sannan babban mai zartarwa a hukumar inshora ta kasa (NAICOM).

Mista Thomas ya maye gurbin Mallam Mohammed Kari, wanda aka nada a matsayin mukaddashin shugaban NAICOM a shekarar 2019.

Buhari ya fara nada Mista Thomas a matsayin mataimakin shuganan hukumar NAICOM mai kula da aiyukan cikin gida a watan Afrilu na shekarar 2017.

Ya na da gogewar aiki ta fiye da shekaru 30 a harkokin da su ka shafi inshora.

Ya taba rike mukamin babban darekta (DG) na kungiyar ma su harkar inshora a Najeriya (NIA) a shekarar 2010.

A wani jawabin da ya fito daga ofishin Yunusa Tanko Abdullahi, kakakin ministan kudi, ya bayyana cewa shugaba Buhari ya sake amincewa da nadin mambobin darektocin zartarwa a hukumar NDIC.

Mambobin biyu da Buhari ya nada sune; uwargida Ya'ana Talib daga yankin arewa maso gabas da uwargida Diana O. Okonta daga yankin kudu maso kudu.

Buhari ya maye gurbin Mallam Mohammed Kari, ya nada sabon shugaban NAICOM

Shugaba Buhari
Source: Twitter

Sanarwar ta ce nadin mutanen ta fara aiki nan take, ba tar da bata lokaci ba.

A jiya Asabar ne Legit.ng ta wallafa rahoton cewa shugaba Muhammadu Buhari ya amince da nadin AVM Muhamadu Alhaji Muhammed (Mai ritaya), a matsayin sabon shugaban Hukumar bayar da agajin gaggawa na kasa (NEMA).

DUBA WANNAN: Dangote ya bawa gwamnatin Kano tallafin cibiyar gwaji ta zamani da babu kamarta a Najeriya

Nadin da aka yi wa Muhammed zai fara aiki ne daga ranar Alhamis 30, ga watan Afrilun 2020 inda zai karbi ragamar mulkin hukumar daga tsohon shugaban ta Injiniya Mustaha Y. Maihaja.

A cewar sanarwar da Direktan watsa labarai na Ofishin sakataren gwamnatin tarayya, Mista Wille Bassey ya fitar a yammacin ranar Asabar, Muhammad zai yi aiki na waadin farko na tsawon shekaru hudu.

Sanawar ta ce, "Nadin za ta fara aiki daga ranar Alhamis 30, ga watan Afrilun 2020 na wa'adin farko na shekaru hudu kamar yadda sashi na 3 na Dokar National Emergency Management Agency Act ta tanada.

"An umurci tsohon shugaban hukumar mai barin gado, Injiniya Mustaha Y. Maihaja ya mika dukkan takardu da bayyanai na ayyuka ga AVM Muhammadu Alhaji Muhammed (Mai ritaya)nan take.

"Shugaban kasar kuma ya mika godiyarsa da shugaban hukumar mai barin gado kana ya bukaci sabon shugaban ya yi aiki tukuru."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel