An sake samun kwayar cutar covid-19 a jikin wasu almajirai 14 da Kano ta mayar Kaduna
Tun bayan barkewar annobar cutar covid a Kano, gwamnatin jihar ta yanke shawarar mayar da almajirai zuwa jihohinsu na asali.
Jihohin Bauchi, Katsina Jigawa da Kaduna na daga cikin jihohin da gwamnatin Kano ta mayarwa almajirai ma su yawa.
An samu kwayar cutar covid-19 a jikin wasu almajirai goma sha hudu da gwamnatin Kano ta mayar jihar Kaduna sakamakon barkewar annobar covid-19.
Kwamishinar lafiya a jihar Kaduna, Dakta Amina Mohammed Baloni, ce ta sanar da hakan a yammacin ranar Asabar.
A cikin satin da ya gabata, Dakta Amina ta ce an samu kwayar cutar covid-19 a jikin wasu almajirai 16 da aka mayar jihar Kaduna daga Kano.
Kafin sanarwar Dakta Amina, gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya sanar da cewa an samu kwayar cutar covid-19 a jikin almajirai 6 da aka dawo da su jihar Bauchi daga Kano.
Dakta Amina ta bayyana cewa alkaluman almajiran da ke dauke da kwayar cutar zai cigaba da hauhawa, saboda har yanzu akwai wadanda sakamakon gwajinsu bai fito ba.
Ta ce an killace dukkan almajiran da aka dawo da su daga Kano domin dakile yaduwar kwayar cutar a jihar Kaduna.
A cewar kwamishinar, gwamnatin jihar Kaduna ta samar da wata na'urar yin gwaji a babban asibitin Yusuf Dantsoho da ke unguwar Tudun Wada a garin Kaduna.
Ta ce za fara gudanar da gwajin kwayar cutar covid-19 a asibitin da zarar hukumar NCDC ta bayar da izini, hakan zai mayar da jimillar cibiyoyin gwaji a Kaduna zuwa guda uku.
Tun ranar 27 ga watan Afrilu, Dakta Baloni ta sanar da cewa an mayar da almajiran zuwa cibiyar duba cututtuka ma su yaduwa, wacce ke zaman cibiyar killacewa ta jihar Kaduna.
DUBA WANNAN: Covid-19: Ku fidda ran daidaituwar al'amura a cikin shekarar nan - Shugaban NCDC
Kazalika, ta sanar da cewa ana duba lafiyar almajiran kamar yadda ake duba lafiyar duk wanda aka tabbatar yana dauke da kwayar cutar a jihar Kaduna.
Ta bayyana cewa an killace sauran almajiran da ake zargin zasu iya harbuwa daga abokansu da aka samu da kwayar cutar, kuma ma'aikatan lafiya na cigaba da sa-ido a kansu.
Kwamishinar ta sake yin kira ga jama'ar jihar Kaduna a kan bukatar su cigaba da biyayya ga matakan kare kai da dakile yaduwar kwayar cutar covid-19.
Kazalika, ta yi kira ga jama'a da su bawa tsafta muhimmanci, sannan suke yawan wanke hannayensu da sabulu.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng