An kama mutumin da ya fallasa jawabin shugaba Buhari – Femi Adesina

An kama mutumin da ya fallasa jawabin shugaba Buhari – Femi Adesina

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi jawabi ga 'yan Najeriya inda ya sanar da ci gaban dokar hana zirga-zirga a jihohin Abuja, Legas da Ogun

- Sa'o'i kadan kafin jawabin, irin jawabin mai cike da kura-kurai ya bazu a kafafen sada zumuntar zamani

- Femi Adesina ya ce wanda ya fitar da jawabin ya shiga hannu kuma tuni yana fuskantar abinda ya dace

Hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Femi Adesina, ya bayyana cewa wanda ya fitar da jawabin shugaban kasa kafin ya gabatar da ita, ya shiga hannu.

Jawabin shugaba Buhari ya bazu cike da kura-kurai tun kafin shugaban kasar ya gabatar da shi a ranar Litinin, 27 ga watan Afirilu.

Amma kuma idan za mu tuna, akwai banbanci mara yawa tsakanin asalin jawabin shugaban kasar da kuma wanda ya bullan.

A wani rubutu da hadimin ya yi wanda yayi masa take da 'Makiyan Najeriya', Adesina ya bayyana cewa an damke wanda ya fitar da jawabin kuma yana karbar abinda ya dace.

"Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi jawabi ga 'yan Najeriya da karfe 8 na daren Litinin a kan yadda ake yakar Covid-19 a kasar nan.

"A nan ne ya sanar da matsaya a kan dokar hana zirga-zirga a babban birnin tarayya, Legas da Ogun. Hankula sun koma kan jihar Kano sakamakon mace-macen da ya tsananta," in ji shi.

A yayin da kasar ke jiran jawabin shugaban kasa, an samu bazuwar yanayin jawabin wurin karfe 4 na yamma.

Kamar yadda hadimin shugaban kasar ya bayyana, kallo daya yasa ya gane cewa jawabin ne da ba a tace ba wani ya fitar.

Ya ce babu shakka wanda ya fitar da wannan jawabin ya yi kutse ne inda ya samo shi.

"Idan wannan ya samu bayanan da za su saka Najeriya cikin wani hali ta hanyar mika su ga makiya, zai yi babu shakka," ya kara da cewa.

Adesina yace a wannan lokacin na fasaha, komai mai sauki ne.

"Kafin yammaci, an bibiyi wanda ya fitar da shi kuma an gano wani mutum da ke da alaka da shi. Yanzu haka yana amsar sakamakonsa," cewarsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel