An kama mutane 204 kan rashin sanya takunkumin fuska a Neja

An kama mutane 204 kan rashin sanya takunkumin fuska a Neja

- Hukumomin tsaro sun kama mutane kimanin su 216 sannan aka hukunta su a kan karya dokar hana fita a jahar Neja

- An kama mafi akasarin mutanen ne sakamakon rashin sanya takunkumin fuska, inda wasu kuma suka yi taro da masu daukar fasinjoji

- Kakakin yan sandan jahar, Wasiu Abiodun ya bayyana cewa an yanke wa masu laifin hukunci daban-daban, ciki harda watanni shida a gidan yari ko biyan tara

Rahotanni sun kawo cewa jami’an tsaro sun kama mutane kimanin su 216 sannan aka hukunta su a kan karya dokar hana fita a jahar Neja. An sallami mutane 12 daga cikinsu.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa mafi akasarin laifukan sun hada da rashin sanya takunkumin fuska yayinda sauran suka tuka ababen hawa a lokacin da dokar hana fitar ke aiki.

An kama mutane 204 kan rashin sanya takunkumin fuska a Neja

An kama mutane 204 kan rashin sanya takunkumin fuska a Neja
Source: Twitter

Sannan wasu sun hada tarurrukan jama’a, wasu kuma sun kwashi fasinjoji a lokacin dokar, da kuma wadanda suka dauki fasinjoji sama da adadin da aka kayyade.

Kakakin yan sandan jahar, Wasiu Abiodun ya bayyana cewa an yanke wa masu laifin hukunci daban-daban, ciki harda watanni shida a gidan yari ko biyan tara.

KU KARANTA KUMA: Likitocin Najeriya 113 sun kamu da cutar coronavirus

A gefe guda mun ji cewa gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya nemi gwamnatin tarayya ta gaggauta sassauta dokar kulle Kano na tsawon sati biyu da ta saka.

Ganduje ya ce ya yi kira a kan a sassauta dokar ne saboda halin matsin tattalin arziki da jama'a ke ciki, musamman a cikin wannan wata na Azumi.

Ganduje ya bayyana hakan ne ranar Alhamis a gidan gwamnatin Kano yayin rantsar da mambobin wani kwamiti da zai taimakawa kwamitin kar ta kwana a kan annobar covid-19 a jihar Kano.

Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatinsa ta na kara fadada aiyukan kiwon lafiya domin samun damar duba adadin ma su dauke da kwayar cutar covid-19, wanda ke cigaba da hauhawa a jihar.

Farfesa Musa Borodo ne shugaban kwamitin da gwamna Ganduje ya rantsar a gidan gwamnatin Kano.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel