Likitocin Najeriya 113 sun kamu da cutar coronavirus

Likitocin Najeriya 113 sun kamu da cutar coronavirus

- Ministan lafiya, Osagie Ehanire ya karyata batun cewa ma'aikatan lafiya 300 sun kamu da cutar corona

- Ehanire ya bayyana cewa likitoci 113 ne kadai suka kamu, kuma mafi akasarinsu sun ito ne daga asibitoci masu zaman kansu

- Ya bayyana hakan a Abuja a ranar Alhamis, 30 ga watan Afrilu, a taron tattaunawa na kwamitin shugaban kasa a kan COVID-19

Ministan lafiya, Osagie Ehanire, ya ce likitocin Najeriya 113, wanda mafi akasarinsu daga asibitoci masu zaman kansu ne, sun kamu da coronavirus.

Ministan ya bayyana hakan a Abuja a ranar Alhamis, 30 ga watan Afrilu, a taron tattaunawa na kwamitin shugaban kasa a kan COVID-19.

Likitocin Najeriya 113 sun kamuda cutar coronavirus

Likitocin Najeriya 113 sun kamuda cutar coronavirus
Source: Twitter

Ya ce: “Game da cewar likitoci 300 sun harbu, wannan tatsuniya ne, ma’aikatan hukumar lafiya basu kamu ba sosai.

"Muna da yawan mutane 113 ne wadanda suka kamu kuma ba dukkansu ne ma’aikatan lafiya na gwamnati ba, mafi yawansu daga asibitocin kudi ne.

“Kuma za ku ji mu koda yaushe a nan muna adawa da kula da masu coronavirus a asibitocin kudi. Muna magana ne da mutanen da ke aikata hakan ba tare da daukar matakan da suka kamata ba.

"Suna sanya wa kansu cutar sannan su je su yada wa iyalansu a gida kuma hakan ba daidai bane.

KU KARANTA KUMA: Allah ya yi wa jarumin Kannywood Ubale Ibrahim rasuwa

“Don haka, ma’aikatan lafiya wadanda basu samu horo ba basu da hurumin kula da masu cutar. Ga wadanda basu da kayayyakin aiki, mun bayyana cewa mun samar da kayan kare kai ya dukkanin mutanen da ke waje.

"Akwai karancin kayan kariya a duniya, kowace kasa na gwagwarmayar samun takunkumin fuska da kayan kariya."

A wani labarin kuma, mun ji cewa akwai yuwuwar samun koma baya a yakar annobar korona a jihar Kano sakamakon ja da baya da likitoci suke yi a asibitin koyarwa na Mallam Aminu Kano.

Likitocin sun koka da rashin kayan kariya, lamarin da suka tabbatar da cewa yana jefe su a hadarin harbuwa da cutar.

Likitocin da ke rukunin masu neman kwarewa a asibitin, sun samu kan su a cikin mawuyacin hali, musamman ta yadda marasa lafiya suke karuwa a asibitin.

Sakamakon samun karuwar mace-mace a jihar, al'amarin na matukar ta'azzara.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel