An gurfanar da wasu maza biyu kan zarginsu da hannu a batan gawar wata mata

An gurfanar da wasu maza biyu kan zarginsu da hannu a batan gawar wata mata

- Wani mai tsaron ma'adanar gawawwaki tare da wani ma'aikaci sun gurfana a gaban wata kotun majistare da ke jihar Ondo

- An gurfanar da mazan biyu ne sakamakon zarginsu da ake da hada kai wurin aikata laifi

- A yayin yanke hukunci, mai shari'a Olubunmi Dosunmu ya bada belin wadanda ake zargin a kan N200,000 kowannensu tare da tsayayyu biyu

An gurfanar da wani mai tsaron ma'adanar gawawwaki tare da wani ma'aikaci a gaban wata kotun majistare da ke jihar Ondo a kan batan gawar wata mata.

Mutanen biyun masu suna, Oladejo Edubi da Samuel Oluwatodimu, sun gurfana ne a gaban kotun da ke Owo a jihar Ondo.

An adana gawar marigayiya Rebecca Ogunoye a ma'adanar gawawwaki da ke asibitin Adeyemi, a yankin Isuada da ke karamar hukumar Owo ta jihar.

An gurfanar da wasu maza biyu kan zarginsu da hannu a batan gawar wata mata
An gurfanar da wasu maza biyu kan zarginsu da hannu a batan gawar wata mata
Asali: Twitter

Kamar yadda jaridar SaharaReporters ta bayyana, an gurfanar da mazan biyu ne sakamakon zarginsu da ake da hada kai wurin aikata laifi.

A yayin bayani a gaban kotun, Owolabi Edu, dan sanda mai gabatarwa ya ce an gudanar da bincike sannan an gano da sa hannunsu a batan gawar.

Ya ce laifin abin hukuntawa ne a karkashin sassa na 517, 242 da 249 na dokokin laifuka na jihar Ondo.

A rokon da suka yi, wadanda ake zargin sun ki amsa laifin da ake zarginsu da shi.

Lauyan wadanda ake kara, Osaze Uwadie ya bukaci a bada belin wadanda ake zargin tare da saka musu sharudda masu tsauri.

A yayin yanke hukunci, mai shari'a Olubunmi Dosunmu ya bada belin wadanda ake zargin a kan N200,000 kowannensu tare da tsayayyu biyu.

Mai shari'ar ta kara da dakatar da asibitin daga karbar gawa har zuwa lokacin da za a kammala shari'ar.

KU KARANTA KUMA: Covid-19: Hukuma ta shiga neman wata mai jego ruwa a jallo bayan sakamakon gwajinta ya fito

Ta kara da umartar cewa a kawo cikakkun sunayen gawawwakin da ke ma'adanar asibitin.

Daga nan ne ta dage shari'ar zuwa ranar 10 ga watan Yunin 2020 don ci gaba da saurare.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel