Cutar Coronavirus ta kashe dan shekara 25 a Lagas

Cutar Coronavirus ta kashe dan shekara 25 a Lagas

- Wani matashi dan shekara 25 ya rasa ransa sakamakon annobar coronavirus a jahar Lagas

- Kwamishinan lafiya na jahar, Farfesa Akin Abayomi, ne ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter

- Abayomi ya ce a lokacin da aka kwantar da marigayin, ya kasance wani mawuyacin hali na numfashi da kyar

Wani mutum mai shekara 25 ya rasa ransa sakamakon annobar coronavirus a jahar Lagas.

Kwamishinan lafiya na jahar, Farfesa Akin Abayomi, ne ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter.

A cewarsa, marigayin, a lokacin da aka kwantar da shi, ya kasance a wani mawuyacin hali na numfashi da kyar.

Yanzu yawan wadanda suka mutu sakamakon cutar COVID-19 a jahar Lagas sun kai 20.

Farfesa Abayomi ya kuma bayyana cewa masu coronavirus a jahar Lagas a ranar 29 ga watan Afrilu sun kasance 947.

Sai dai kuma, ya nuna farin ciki a kan sallamar wasu karin mutane 49 da suka warke a ranar Laraba, 29 ga watan Afrilu.

Yanzu jimlar mutane 187 kenan aka sallama a jahar.

Ya bukaci mazauna jahar da su ci gaba da bin matakan da aka tanadar domin kare kai daga kamuwa da cutar.

KU KARANTA KUMA: Wasu masu bincike a Najeriya sun sanar da samun maganin cutar covid-19

A wani labarin kuma, mun ji cewa kwamishinan lafiya na jahar Lagas, Farfesa Akin Abayomi, ya ce cutar Coronavirus na shafar lafiyar koda da jinin dan Adam.

Ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, 29 ga watan Afrilu a lokacin wani shirin Arise News.

Kwamishinan ya yi gargadin cewa masu kitse a jiki, da ciwon suga da hawan jini su yi hankali sosai, domin halin da suke ciki ka iya haifar da kamuwa da mummunar cutar.

“Akwai sabbin abubuwa da aka gano game da annobar COVID-19. Misali, ba wai cutar lumfashi bace kawai kai tsaye. Mun gano cewa yana shafar jini da koda.

“Wadanda abun zai fi shafa sune masu ciwon suga, hawan jini da matsalolin garkuwar jiki. Masu kitse a jiki ma na cikin hatsari. Idan ka fada cikin kowani rukuni, ya zama dole ku yi taka-tsan-tsan,” in ji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng