Gwamnan Bauchi ya amince da wata kwayar bature domin maganin cutar covid-19

Gwamnan Bauchi ya amince da wata kwayar bature domin maganin cutar covid-19

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya amince da amfani da allurar kwayar sinadarin 'chloroquine' da 'zithromax' a matsayin maganin kwayar cutar covid-19.

Bala Mohammed, wanda shine mutum na farko da ya fara kamuwa da kwayar cutar covid-19 a jihar Bauchi, ya ce da magungunan biyu aka yi amfani a kansa har ta kai ga ya samu sauki.

Gwamnan ya bayyana hakan ne ranar Laraba yayin wani taro a kan annobar covid-19 da aka yi a gidan gwamnatin jihar Bauchi.

A cewar gwamnan, "bana son kowa ya mutu, a saboda haka zan dauki alhakin duk abinda zai faru sakamakon amfani da magungunan."

"Duk da ba a yarda da amfani da magunguna a wasu wuraren ba, likitocinmu zasu yi amfani da kwarewarsu da gogewarsu wajen amfani da magungunan biyu a kan masu dauke da cutar covid-19 a Bauchi," a cewarsa.

A jawabinsa ga tawagar kwararru a bangaren kiwo lafiya, gwamnan ya ce, "na baku umarnin yin amfani da magungunan a kan masu dauke da kwayar cutar, kamar yadda aka yi amfani da su a kaina har na samu waraka

Gwamnan Bauchi ya amince da wata kwayar bature domin maganin cutar covid-19
Gwamnan Bauchi; Bala Mohammed
Asali: UGC

"Ba zamu zauna mu ce wani abu yana da illa ba, saboda kawai turawa sun bayyana hakan, ba zamu bar mutane haka ba tare da yin kokari na ceto rayuwarsu ba.

"Mun saba amfani da 'chloroquine' a Najeriya. Zamu cigaba da amfani da ita. Na dauki alhakin duk wani abu da zai biyo baya.

"Zithromax da Chloroquine basa yi wa jikinmu wata illa, yanayin jikinmu ya saba da ita. Da chloroquine muke amfani duk lokacin da muke fama da zazzabi."

DUBA WANNAN: Kasa da sati uku, Kano ta koma mataki na biyu a yawan masu cutar covid-19 a Najeriya

Gwamnan ya kara da cewa sakamakon amfani da kwayoyin biyu ne yasa har yanzu babu wanda cutar covid-19 ta kashe a jihar Bauchi.

A kwanakin baya ne masana kimiyyar lafiya suka caccaki shugaban kasar Amurka, Donald Trump, bayan ya sanar da cewa ya amince da amfanin 'chloroquine' da 'Zithromax' domin maganin cutar covid-19.

Kazalika, hukumar kula da lafiya ta duniya (WHO) ta yi watsi da maganar amfani da magungunan biyu waje maganin cutar covid-19.

WHO ta ce magungunan basu bi matakan tabbatar da tasirin magunguna kafin amfani da su domin maganin wata cuta ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng