Kaduna: El-Rufai ya bayyana dalilin zabtare albashin ma'aikatan jihar

Kaduna: El-Rufai ya bayyana dalilin zabtare albashin ma'aikatan jihar

- Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya bayyana dalilin da yasa ya zabtare albashin ma'aikatan jihar

- A yayin bayani a kan hukuncin, El-Rufai ya ce an yi hakan ne don samar da mafita ga mabukatan jihar

- Gwamnan ya ce akwai sama da mutum miliyan daya a jihar da ke fita kullum don neman abinci amma hakan ya gagara saboda kulle

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya bayyana dalilin zabge albashin ma'aikata da masu mukaman siyasa na jihar.

Ya ce hakan zai taka rawar gani wurin tallafawa mabukata tare da tabbatar da walwalar mazauna jihar.

El-Rufai ya ce gwamnatin ta yanke hukuncin zabge albashin ma'aikatan jihar ne don su taimaka wajen bada tallafin rage radadi ga wadanda basu da hali.

Gwamnan wanda ya sanar da hakan a yayin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai a shirin kai tsaye da aka yi dashi a ranar Talata, 28 ga watan Afirilun, yace gwamnatin jihar bata da wata matsala a fannin biyan albashi.

Kamar yadda El-Rufai ya bayyana, sama da mutum miliyan daya da ke jihar na fita ne kullum don samun abinda za su ci, amma hakan ya gagara saboda dokar hana zirga-zirga da aka saka a jihar.

El-Rufai ya ce gwamnatin jihar ta yanke hukuncin zabtare N500,000 daga albashin 'yan majalisar zartarwar jihar don samar da kayan rage radadi.

Kaduna: El-Rufai ya bayyana dalilin zabtare albashin ma'aikatan jihar
Kaduna: El-Rufai ya bayyana dalilin zabtare albashin ma'aikatan jihar
Asali: UGC

DUBA WANNAN: COVID-19: El-Rufai ya bada sharudda 3 na sassauta doka a jihar Kaduna

"A don haka ne muka yanke hukuncin cewa mu rage daga albashin ma'aikata don gwamnati ta samu damar kyautatawa jama'ar jihar.

"Daga yanzu za mu ci gaba da sadaukar da rabin albashinmu har zuwa lokacin da rayuwa za ta koma daidai," gwamnan yace.

Amma kuma, an gano cewa ma'aikatan gwamnati masu albashi daga N67,000 zuwa sama ne za su sadaukar da kashi daya bisa hudu na albashinsu don samar da kayayyakin rage radadi ga mabukata.

El-Rufai yace: "Addinanmu an koyar da mu tausayi da jin kai ga jama'a kuma mu so wa 'yan uwanmu abinda muke so wa kanmu.

"Idan kana da damar albashi a wannan lokacin, ka tallafawa na kasa da kai don su samu damar rayuwa a yayin wannan annobar."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel