Wasu masu bincike a Najeriya sun sanar da samun maganin cutar covid-19

Wasu masu bincike a Najeriya sun sanar da samun maganin cutar covid-19

Wata kungiyar masu bincike a jihar Edo ta ce ta samar da magani takamaimai na cutar COVID-19.

Pax Herbal Clinic and Research Laboratories ya ce maganin mai suna CVD PLUS na kunshe da tsirrai ne da sinadarai wadanda suke iya inganta garkuwar jiki don yakar Coronavirus.

"Paxherbals ta yi nasarar samo maganin cutar coronavirus mai suna CVD PLUS, an hada shi ne takamaimai don maganin cutar.

"Maganin na kunshe da tsirrai wadanda masana kimiyya suke amfani dasu tun shekaru 25 da suka gabata wajen magance cututtukan hanta, kanjamau, lamonia da zazzabin cizon sauro," dakin gwajin ya sanar.

Wasu masu bincike a Najeriya sun sanar da samun maganin cutar covid-19
Wasu masu bincike a Najeriya sun sanar da samun maganin cutar covid-19
Asali: Twitter

Wasu daga cikin sinadaran da aka hada maganin dashi na da karfin habbaka garkuwar jikin, tare da samar da sinadarai a cikin jini da za su iya halaka kwayar cutar coronavirus.

Dakin gwajin wanda suka yi ikirarin ya kafu tun a 1996, an kafa shi ne don habbakawa tare da inganta magunguna a nahiyar Afrika.

Masu binciken sun yi ikirarin cewa wasu wakilan manyan cibiyoyin gwamnati da suka hada da NAFDAC sun taka rawar gani wurin hada maganin.

Hakazalika, Ese Osezuwa wanda shine jami'in yada labarai na dakin gwajin, ya sanar a ranar Alhamis cewa, har yanzu dai basu yi wa maganin gwajin inganci ba a kan mai dauke da cutar coronavirus.

Jaridar The Cable ta tuntubi hukumar NAFDAC da cibiyar masu bincike ta kasa, wacce kungiyar ta ce sun san da maganin, amma dukkansu sun tabbatar da babu wani maganin gargajiya da aka tabbatar yana yakar cutar.

NIMR ta ce a halin yanzu tana nazarin maganin a daya daga cikin cibiyoyinta.

Daraktan yada labarai na ma'aikatar lafiya na jihar, Eenfaa Bob-Manuel, ya sanar da The Cable cewa babu wanda ya sanar da ma'aikatar komai a kan maganin.

Amma kuma a takardar da Pax Herbal ta fitar wacce Anselem Adodo ya saka hannu a madadin ta, ta ce maganin da aka samo daga tsirrai ne kadai zai iya magance kwayar cutar.

Amma kuma har yanzu babu wata hujja a kimiyyance da ta tabbatar da hakan.

Cibiyar kiwon lafiya ta duniya ta ja kunnen jama'a a kan kirkirar magani tare da sha don magance cutar.

KU KARANTA KUMA: Mace-macen Kano: Kashi 41 cikin 100 sun nuna alamun COVID-19 - Sabon Bincike

Mun ji cewa gwamnatin tarayya ta ce za ta tunkari kasar Madagascar don karbar maganin gargajiyar da suke amfani da shi wurin magance cutar coronavirus.

Gwamnatin tarayyar ta sanar da hakan ne bayan kasar ta kaddamar da wani maganin gargajiya wanda tace yana kawo sauki a yayin jinyar cutar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel