Trump: Mun fi kowace kasa yin gwaji, shiyasa mu ke da yawan masu COVID-19

Trump: Mun fi kowace kasa yin gwaji, shiyasa mu ke da yawan masu COVID-19

Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya sake yin magana game da annobar Coronavirus da ta addabi kasarsa. Trump ya bayyana abin da ya sa Amurka ta fi kowa fama da masu cutar.

Shugaba Donald Trump ya ce ana samun labarin masu dauke da cutar COVID-19 sosai a kasar Amurka ne kawai saboda ana yawan yi wa mutanen kasar gwajin wannan muguwar cuta.

Donald Trump ya fito shafinsa na Tuwita a jiya ya na cewa sauran kasashen Duniya ba su da labarin masu dauke da cutar COVID-19 ne saboda karancin adadin wadanda ake yi wa gwaji.

Trump ya ce: “Abin da kawai ya sa kasar Amurka ta ke da labarin mutane miliyan guda da su ka kamu da Coronavirus shi ne saboda karfin yin gwajin mu ya fi na kowace kasa a Duniya.”

Shugaban Amurkan a rubutun na sa ya ce: “Sauran kasashe su na bayanmu sosai wajen yin gwajin kwayar cutar COVID-19. Don haka wannan ya sa su ke bada adadin da bai kai namu ba.”

KU KARANTA: Trump ya kira Shugaba Buhari a kan batun annobar Coronavirus

Mista Trump wanda ya yi suna a dandalin Tuwita ya kara da cewa ‘yan jarida ba su ganin kokarin da gwamnatin Amurka ta ke yi a wannan fanni da ma wajen samar da na’urorin asibiti.

“Duk da haka gidajen yada labarai ba su kokawa. Duk irin abin kirkin da mu ka yi, haka abin ya ke wajen na’urorin taimakawa numfashi, ba za su taba cewa mu na abin a yaba ba.” Inji Trump.

Shugaba Trump ya ce abin da ‘yan jarida kawai su ke yi shi ne kushe kokarin Amurka. Kwanaki Trump ya zaburar da kamfanoni su dage wajen hada na’urorin da ke agazawa numfashi.

A yau Alhamis kuma Donald Trump ya shiga sukar kasar Siwidin a game da matakin da ta dauka na kin rufe kasar. Ya ce dalilin haka ne aka samu mutane 2,400 sun mutu a rana daya a kasar.

Jaridar Punch ta ce a gida Najeriya an yi wa mutane kimanin 10, 000 gwajin wannan cuta inda aka samu mutum fiye da 1, 5000 dauke da ita. Ana so a rika yi wa mutane 2, 500 gwaji duk rana.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng