Annobar covid-19 ta ci rai na farko a jihar Jigawa

Annobar covid-19 ta ci rai na farko a jihar Jigawa

Annobar cutar covid-19 ta ci ran mutum na farko a jihar Jigawa, yayin da jimillar ma su dauke da kwayar cutar a jihar ya kai mutane tara.

Kwamishinan lafiya a Jigawa, Dakta Abba Zakari, ne ya sanar da hakan yayin gabatar da jawabi ga manema labarai a matsayinsa na shugaban kwamitin kar ta kwana na jiha a kan annobar covid-19.

Da ya ke sanar da hakan a Dutse, babban birnin jihar Jigawa, kwamishinan ya ce an kara rufe wasu kananan hukumomi hudu; Dutse, Gwaram, Miga da Auyo.

Kananan hukumomin za su bi sahun kananan hukumomin Kazaure, BirninKudu, da garin Gujungu a karamar hukumar Taura, wadanda gwamnatin jiha ta sanar da rufesu a baya.

A cewar kwamishinan na lafiya , babban kalubalen da jihar Jigawa ke fuskanta shine na rashin dakin gwajin kwayar cutar covid-19, amma ya ce gwamnati na tattaunawa da wani dakin gwaji mai zaman kansa da NCDC ta yarda da shi.

Sai dai, Dakta Zakari bai bayar da karin bayani a kan mutumin da cutar covid-19 ta kashe ba, kazalika bai ambaci a ina ya mutu ba.

Annobar covid-19 ta ci rai na farko a jihar Jigawa
Gwamnan jihar Jigawa; Badaru Abubakar
Asali: Twitter

Kafin sanarwar Dakta Zakari, Legit.ng ta wallafa cewa gwamnatin jihar Jigawa ta sanar da rufe wasu kananan hukumominta guda uku bayan samun bullar annobar covid-19.

A ranar Talata ne hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa ta kasa (NCDC) ta sanar da cewa sabbin mutane 195 sun kamu da kwayar cutar covid-19. Biyar daga cikin mutanen sun fito ne daga jihar Jigawa.

DUBA WANNAN: A karshe, sojojin Najeriya sun kwace kauyen Bula Shatana, 'yan Boko Haram sun mika wuya

Da yake sanar da rufe kananan hukumomin guda uku, gwamnan Jigawa, Badaru Abubakar, ya ce an samu karin mutane biyu da suka kamu da kwayar cutar covid-19 a jihar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da yake gabatar da jawabi ga manema labarai a gidan gwamnatin Jigawa da ke Dutse, babban birnin jiha.

A cewar Badaru, an tabbatar da samun kwayar cutar covid-19 a jikin wani mutum mazaunin garin Gujungu a karamar hukumar Taura.

Dayan kuma da aka samu yana dauke da kwayar cutar, dan asalin karamar hukumar Birnin Kudu ne amma yana aiki a karamar hukumar Gumel, lamarin da yasa dokar kullen ta shafi kananan hukumomi uku.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng