WFP ta ce za ayi fama da rashin abinci a Sudan, Kenya, Uganda da wasu kasashe 6
Annobar cutar COVID-19 ta yi barna a kasashen Duniya da-dama. Ta’adin da wannan cuta ta yi ya shiga Afrika har ma an fara hasashen za ayi fama da mugun karancin abinci a yankin.
Majalisar dinkin Duniya ta yi gargadi cewa rashin abinci zai yi kamari a cikin wata uku a wasu kasashen Afrika. UN ta bayyana wannan ne a jiya ranar Talata, 28 ga watan Afrilu, 2020.
A cewar majalisar dinkin Duniya akwai mutane akalla miliyan 20 da ba su da isasshen abinci a Nahiyar ta bakaken fata. Babu sunan Najeriya a cikin rahoton da majalisar ta fitar jiya.
Kasashen da ake hasashen za su yi fama da yunwa sun hada da Burundi, Djibouti, Habasha, Eriteriya, Kenya, Ruwanda. Sauran kasashen su ne Somaliya, da kuma Kudancin Sudan.
Uganda wanda ita ma ta ke yankin gabashin Afrika ita ce ta tara a wannan jeri. Wadannan kasashen ba su cikin inda annobar Coronavirus ta yi wa mummanan kamu a halin yanzu.
KU KARANTA: An kusa bude masallatan harami domin a cigaba da ibada a Saudi
Duk da cewa masu dauke da cutar COVID-19 ba su da yawa a kasashen nan, sai dai yanayin rashin karfin tattalin arzikinsu da kuma halin da asibitocinsu su ke ciki zai jefa su a matsala.
“Hukumar World Food Program ta Duniya ta yi hasashen cewa wadanda ba su da abinci a wannan yanki za su tashi daga miliyan 34 zuwa mutum miliyan 43 nan da watanni uku.”
“Idan abin ya jagwalgwale halin da za a shiga zai fi haka muni, wadanda ba su da abinci za su ribanya biyu a dalilin annobar COVID-19.” Elisabeth Byrs ta fadawa ‘yan jarida haka jiya.
Mai magana da yawun hukumar watau Misis Byrs ta ce WFP ta na bukatar fiye da dala miliyan 500 nan da watanni uku a yankin na gabashin Afrika a daidai wannan mawuyacin hali.
“Ba wai matsalar rashin samun abinci ba ne ta sanadiyyar kwarin gona da fari, ko kuma matsalar kudi saboda rugurgujewar tattalin arziki, matsalar duka wadannan ce gaba daya.” inji ta.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng