An kusa bude Masallatan Harami - Sheikh Sudais
Shugaban Masallatan Harami na Makkah da Madina, Sheikh Abdurrahman Sudais, ya sanar da cewa an kusa a bude masallatan guda biyu domin ci gaba da yin ibada a cikin su.
Ya sanar da hakan ne a cikin wata wallafa ta bayar da kwarin gwiwa da ya yi a ranar Talata kan shafin Masallatan na Facebook Haramain Sharifain.
Cikin bidiyon da shafin na Haramain Sharifain ya sanya a Facebook, Sheikh Sudais yana cewa: "Lokacin da fargaba za ta gushe daga zukatan al'ummar musulmi ya gabato, domin nan ba dadewa zamu bude masallacin Makkah domin a ci gaba da gudanar da dawafi da Safa da Marwa.
"Haka kuma zamu bude masallacin Annabi Muhammad da ke birnin Madina domin a ci gaba da kai ziyara."
Sheikh Sudais ya ci gaba da cewa: "Komai zai dawo kamar yadda yake a baya da yardar Allah Mai Bada Iko a kan komai."
An ruwaito ma'aikatar kula da ayyukan Hajji da Umrah ta ne cewa, "da izinin Allah, karkashin jagoranci gwamnatinmu, da kuma kiyaye umarnin hukumomi, abubuwa za su dawo tamkar yadda suka a baya garin na Makkah da kuma kai ziyara Masallacin Madinah."
Kamar yadda jaridar Saudi Gazette ta wallafa, Sheikh Sudais ya jagoranci dashen kyamarorin tsaro a Masallatan Haramin guda biyu, wadanda za su taimaka wajen gano duk mai dauke da wannan cuta ta korona.
KARANTA KUMA: Cutar korona ta harbi mutane 34,000 a nahiyyar Afirka - WHO
An sanya wadannan na'urorin daukar hoto ne a daidai kofar shiga Masallatan da ke Makkah da Madina, inda a lokaci guda za su iya gano yanayin zafin jikin kimanin mutane 25.
Sai dai duk da hakan, babu tabbacin yiwuwar gudanar da aikin hajji a bana, sanadiyar yadda gwamnatin Saudiya ta nemi kasashen duniya su jingine karbar kudin maniyyatan bana.
Gwamnatin Saudiya ta dauki wannan mataki ne a sanadiyar yadda likafar annobar cutar korona ta ke ci gaba a fadin duniya.
A ci gaba a fafutikar dakiile yaduwar cutar korona, tuni dai mahukuntan Saudiya suka hana shiga manyan garuruwan kasar da suka hadar da Makka, Madinah da kuma Riyadh, babban birnin kasar.
Alkaluman hukumomin lafiya na Saudiya sun tabbatar da cewa ya zuwa yanzu, cutar korona ta harbi mutane 1,325, kuma kaso 85% daga cikinsu baki ne a kasar.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng