Albashi: Mu na tara N2b kowane wata a jihar Imo – Gwamna Hope Uzodinma

Albashi: Mu na tara N2b kowane wata a jihar Imo – Gwamna Hope Uzodinma

Bayan watanni uku da rabi a ofis, gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma ya bayyana irin tasirin da ake gani a gwamnati a sakamakon gyare-gyaren da ya kawo daga Junairu zuwa yanzu.

Gwamna Hope Uzodinma ya bayyana cewa daga lokacin da ya dare kan mulki zuwa wannan lokaci, matsakaicin abin da ya ke adanawa a asusun Imo duk wata ya kai Naira biliyan biyu.

Hope Uzodinma ya yi wannan jawabi ne sa’ilin da ya ke bayyana irin kokarin da ya yi cikin kwanaki 100 na farko da ya yi a mulki. Uzodinma ya zama gwamna ne a tsakiyar Junairu.

Mai girma gwamnan ya ke cewa: “Abin da wannan ya ke nufi shi ne gwamnati za ta samu kudin yin hanyoyi, gina gidaje, inganta asibitoci da kuma makarantu a 'yan shekaru masu zuwa.”

Gwamnan ya bayyana wannan ne a ranar Litinin da ya zanta da manema labarai a babban birnin jihar Imo na Owerri. Gwamnan ya ce zai yi amfani da wannan kudi wajen kawowa Imo cigaba.

KU KARANTA: Yadda na shafe kwanaki 26 a killace bayan na kamu da COVID-19

Albashi: Mu na tara N2b kowane wata a jihar Imo – Gwamna Hope Uzodinma

Sanata Hope Uzodinma ya ce zai yaki masu ci da gumin mutanen Imo
Source: Facebook

“Bari in yi amfani da wannan dama in roki mutanen jihar Imo masu daraja da su bi tafiyarmu ta bankado mugayen mutanen da ke satar kudin baitul-malin jama'a ta badakalar albashi.”

A jawabin na sa gwamnan ya tabbatar da cewa zai rika biyan ma’aikata albashinsu kafin kowane karshen wata. Sai dai gwamnan ya ce ba zai bari a rika karkatar da kudin bayin Allah ba.

“Yayin da na ke da niyyar cika alkawarin da na yi, ba zan bari wasu miyagu su sa in rika biyan albashi ga ma’aikatan bogi ba, wanda a karshe kudin ya ke karewa a cikin aljihunsa.”

Sanata Hope Uzodinma ya kara da neman hadin kai wajen ganin bayan barayi: “Za mu yi bakin kokarinmu wajen gano duk wata kadarar gwamnatin Imo da wani ko wasu su ka karkatar.

“Mutanen jihar Imo su yarda cewa za mu karbe duk wasu kadarorin gwamnati da ke hannun tsirarun mutane, kuma ko wanene mu ka samu da hannu a ciki.” Inji Gwamnan na APC.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel