COVID-19: Mahaifiyata ta umurce ni da na aske gemuna bayan na warke – El-Rufai

COVID-19: Mahaifiyata ta umurce ni da na aske gemuna bayan na warke – El-Rufai

- Gwamna Nasir El-Rufai na jahar Kaduna ya ce mahaifiyarsa ta bukaci da ya aske gemunsa bayan ya warke daga mummunar cutar coronavirus

- Gwamnan ya ce mahaifiyarsa ba ta san ya kamu da COVID-19 ba amma an dai fada mata cewa bashi da lafiya

- El-Rufai ya ce tsawon wata guda bai aske gemunsa ba sannan cewa har ya fara sabawa da shi, amma mahaifiyarsa ta yi masa umurnin aske shi

Gwamna Nasir El-Rufai na jahar Kaduna ya bayyana yadda suka kwashe da mahaifiyarsa bayan ya warke daga mummunar annobar coronavirus.

A cewar gwamnan, mahaifiyarsa ba ta san ya kamu da cutar coronavirus ba illa kawai ta san cewa bashi da lafiya, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

COVID-19: Mahaifiyata ta umurce ni da na aske gemuna bayan na warke – El-Rufai

COVID-19: Mahaifiyata ta umurce ni da na aske gemuna bayan na warke – El-Rufai
Source: Depositphotos

Legit.ng ta ruwaito cewa gwamnan ya ce: “Na je wajenta sanye da takunkumin fuska sannan ta nemi sanin dalilina na sanya takunkumin fuska don haka sai na fada mata cewa wani mataki ne a kan coronavirus.

"Ta tambaye ni dalilina na sanya takunkumin alhalin bani da cutar, hakan ya kasance ne saboda ba a fada mata na harbu ba, an dai fada mata bani da lafiya, a lokacin ne na fada mata cewa na yi fama da rashin lafiya amma na warke.”

A cewar El-Rufai, ya bi umurnin mahaifiyarsa sannan ya cire takunkumin fuskarsa. Sai ta tambaye shi: “menene wannan?”

Gwamnan ya ce: “Sai na fada mata cewar ban yi aski ba tsawon wata guda sannan a nan take ta nemi na aske shi sannan ta tunatar da ni cewa mahaifina bai bar gemu ba har zuwa mutuwarsa sannan cewa idan yayana bai bar gemu ba me ya sa ni na bari?”

KU KARANTA KUMA: PDP ta yi wa El-Rufai wankin babban bargo a kan tsawaita rufe Kaduna na tsawon kwanaki 30

El-Rufai ya ce ya so barin gemun saboda ya riga ya saba da shi, amma dole ya bi umurnin mahaifiyarsa domin ya rabu da ita lafiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel