Gangancin Jami’an tsaro ya sa cutar COVID-19 ta ke yaduwa sosai a Ondo – Akeredolu

Gangancin Jami’an tsaro ya sa cutar COVID-19 ta ke yaduwa sosai a Ondo – Akeredolu

Gwamnan jihar Ondo Oluwarotimi Akeredolu ya fito gaban 'yan jarida, ya na cewa gangancin jami’an tsaro ya taimaka wajen yawaitar masu dauke da cutar COVOID-19 a jiharsa.

Mai girma Rotimi Akeredolu ya bayyana wannan ne a lokacin da ya gana da manema labarai a ranar Talata, 28 ga watan Afrilu, 2020. Gwamnan ya yi wannan ganawa ne a birnin Akure.

Gwamnan na Ondo ya yi wa mutanensa jawabi bayan an samu mutane takwas da su ka kamu da Coronavirus. Gwamnan ya ce an samu karin masu wannan cuta ne a karshen makon jiya.

“Mutum na hudu da na biyar da aka samu dauke da cutar, jami’an ‘yan sanda ne daga Legas, wannan ya nuna cewa akwai ganganci da sabawa doka da ko oho kan halin lafiyar jama’a.”

“Mutum na hudu da aka samu da cutar ‘dan sanda ne da ke zama a Legas. Bayan ya fahimci ya na dauke da alamun ciwon, sai ya je aka yi masa gwaji a Yaba, aka ce ya jira sakamakonsa.”

KU KARANTA: Gwamna Akeredolu ya ragewa masu rike da kujerun gwamnati albashi

Gangancin Jami’an tsaro ya sa cutar COVID-19 ta ke yaduwa sosai a Ondo – Akeredolu
Gwamna Akeredolu ya ce Jami'an tsaro su ka ba COVID-19 mafaka a Ondo
Asali: Depositphotos

“Bayan kwana biyu (ranar Laraba), ba tare da ya karbi sakamakon gwajinsa ba, sai ya kamo hanya zuwa Akure inda iyalinsa su ke. A ranar Alhamis aka fada masa ya na dauke da cutar.”

“Sai ya koma Legas a ranar Alhamis, ya yi ikirarin cewa ya kira malaman lafiya amma ba su zo ba, ya sake dawowa Akure a ranar Asabar dauke da mutum na biyar da ya kamu da cutar.”

“An yi maza an gane halin lafiyarsa, sai aka kwantar da shi (na biyar) a asibitinmu na kula da wadanda su ka kamu da cututtuka masu yaduwa inda yanzu ake kula da shi.” Inji gwamnan.

Akeredolu ya ce mutum na shida da aka samu da cutar wani ne da ake zargi da laifin kisan kai. Ya ce mutum na bakwai da ke da cutar mace ce da ta saci hanya ta shigo Ondo daga Abuja.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel