Sai karshen shekarar 2021 maganin da zai warkar da COVID-19 zai samu

Sai karshen shekarar 2021 maganin da zai warkar da COVID-19 zai samu

Wani fitaccen masanin lafiya a kasar Turai, Pasi Penttinen ya yi karin haske a kan lokacin da za iya samun maganin cutar COVID-19. Masanin ya nuna cewa Duniya ta na da sauran jira.

Pasi Penttinen wanda babban mai bincike da nazari ne a Duniya ya ce sai zuwa karshen shekara mai zuwa watau 2021 za a samu maganin cutar Coronavirus da ta kashe mutane 217, 000.

Penttinen ya ce idan an yi dace za a iya samun maganin wannan cuta nan da shekara daya da rabi. Wannan masani ya shaidawa gidan talabijin na Sky News cewa hakan ma sai an taki sa’a.

A cewar Pasi Penttinen, hada sabon magani ya na daukar lokaci sosai, sannan kuma ya ce abu ne mai wahalan gaske, tare da matukar cin kudi. Bayan haka sai an dauki lokaci ana yin gwaji.

Mista Penttinen ya fadawa ‘yan jarida cewa kafin a iya tabbatar da ingancin maganin wata cuta, dole sai an yi gwaji a kan mutane, ta haka ne kawai za a fahimci ko maganin zai iya yin aiki.

KU KARANTA: Har yanzu babu lokacin da za a koma makaranta a Najeriya

Sai karshen shekarar 2021 maganin da zai warkar da COVID-19 zai samu

Penttinen ya ce sai an yi sa'a za a samu maganin COVID-19 a badi
Source: Twitter

“Sai cikin ikon Ubangiji za a iya samun magani a cikin shekara daya da rabi.” Pasi Penttinen shi ne shugaban wata cibiya ta ECDC mai nazari a kan cututtukan sanyi da numfashi a Turai.

A halin yanzu wannan masani ya karkatar da hankalinsa wajen gano kwayan maganin da zai iya warkar da Coronavirus. Mutane fiye da miliyan uku su ke fama da wannan cuta a Duniya.

Dole sai an yi ta faman gwaji iri-iri bayan an kirkiro maganin da ake sa ran zai kashe kwayar cutar. Idan an yi nasarar warkar da cutar daga jikin maras lafiya ne za a kai maganin kasuwa.

Daga yanzu zuwa karshen shekara mai zuwa za a kara samun dubban mutane wanda wannan cuta zai hallaka a kasashe. Babu mamaki kuma a gano wani maganin kafin wannan lokaci.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel